Alhussain Suleiman" />

An Ya Ba Wa Gwamnatin Kano Kan Kokarin Ta Na Dakile Cutar Korona

Gwamnatin Kano

An ya ba wa gwamnatin jihar Kano a karkashin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, akan kokarin ta take yi wajen kawo karshen dakile cutar korona a fadin jihar Kano, matukar aka cigaba da kiyaye wannan da yardar Allah cutar za ta zama tarihi, sannan zaman da gwamnan ya yi da kungiyoyin ‘yan kasuwar akan dakile cutar zai taimaka sosai. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar masu gidaje dake kasuwar antin kwari dake Kano, Alhaji Balarabe Tatari a lokacin da yake zantawa da manema labarai akan sake bullar cutar ta korona karo na biyu.

Alhaji Balarabe Tatari, y ace ba bu shakka karfafa yin anfani da takunkumin rufe fuska ga gwamnatin ta karfafa yin amfani da shi zai taimaka wajen dakile cutar .Ganin yadda zaman gida da aka shiga a wancan lokacin ya tayar da hankulan al’umma , ya na da kyau al’umma su cigaba da bin dokokin ka da asake rufe garin Karo na biyu . Amatsayin shin a shugaban kungiyar suna cigaba da raba takunkumin rufe fuska da kuma bokitan wanke hannu adaukacin gidajen dake karkashin kulawar kungiyar. Daga karshe ya yi amfani sa wannan dama da rook ga gwamnan na jihar kano , cewa ya rika zama da kugiyar su akan duk wani abu day a shafi harkokin kasuwanci a kasuwar ta kwantin kwari, saboda wasu lokutan ba samun sakon da aka aiko daga wurin gwamnan

 

Exit mobile version