Daga Mukhtar Yakubu A Kano
Fitaccen dan Gwagwarmaya kuma jagoran tafiyar da Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, Musa Abdullahi Sufi, mutum ne da ya kasance mai fafutukar ganin al’umma sun samu kyakyawar rayuwa musamman ma masu karamin karfi, ya shafe tsawon shekaru yana hidumtawa jama’a, domin ganin kwarewar sa ne ma har ta kai shi ga a yanzu aka dora masa alhakin tafiyar da Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wadda Gidauniyar ta yi fice a wannan lokacin wajen bayar da gudummawa ga mabukata musamman ta bangaren ilimi da kuma Lafiya. Domin jin yadda ya samu kan sa a matsayin don Gwagwarmaya da kuma irin gudummawar da Gidauniyar da ya ke jagoran ta a yanzu ta ke bayar da tallafi ga mabukata. MUKHTAR YAKUBU, ya tattauna da shi don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.
Da farko za mu so ka yi wa masu karatun mu yadda ka fara wannan harka ta ka ta bayar da tallafi ga mabukata.
To ita wannan harka ta faro ne tun daga abin da aka ga iyaye suna yi ta wajen bayar da gudummawar su da kuma tallafawa mabukata, ta haka ne muka fara suna karfafa mana gwiwa, don ba na mantawa kullum abin da iyaye su ke fada mana shi ne abin da su kadai zai amfane su kada Allah ya ba su, don haka sun fi son abin da za su amfana kowa ma ya amfana da shi, to a kan irin wannan aka dora mu, don haka abin ya yi tasiri a gare mu, sosai tare da kuma kallon wasu zakakuran mutane da su ke da irin wannan dabi’a ta tallafawa mabukata, kuma ko addini ma abin da ya dora mu a kai kenan domin idan ka kalli rayuwar Manzon Allah haka ya tafiyar da rayuwar sa. Kuma yawon da na yi a kasashen duniya na nuna mini ba mu kadai muke da irin wannan ba don haka sai na ga akwai bukatar na samar da irin wannan yanayi na tallafa wa jama’a. Sai kuma a yanzu na samu kaina a matsayin jagoran tafiyar da Gidauniyar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.
Ita wannan Gidauniya ta Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanne bangare ta fi baiwa muhimanci wajen bayar da tallafin da ta ke yi?
To ita wannan Gidauniyar ta fi bayar da muhimanci ga bangaren ilimi, Lafiya, da kuma hakkin Jama’a, da samar da ruwan sha, ka ga wannan duk suna kan gaba wajen abin da marassa shi suka fi bukata, sai kuma wadanda Matsaloli. To ita wannan Gidauniyar ta Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo tana ba su tallafi amma dai ka sani duk wani tallafi da a ke bayarwa yana fitowa ne daga shi wanda ya samar da ita.
Da ka yi maganar ilimi sai muka ga ilimi yana da bangarori da yawa, tun daga matakin firamare har zuwa Jami’a kuma kowanne yana bukatar taimako, wanne ku ka fi baiwa muhimanci?
Mu a bangaren ilimi ko’ina muna tabawa tun daga firamare don ka ga akwai firamare da aka gina wada aka ba ta sunan Adamu Abubakar Gwarzo. Sannan kuma akwai makarantun firamare da muka inganta su a garin Gwarzo, sai tallafin karatu da a ke bayarwa ga dalibai da su ke da kwazo, sai kuma wadanda ba su da shi, domin a yanzu maganar da na ke yi maka akwai sama da mutane 200 da suka samu tallafin, wasu ma sun samu aiki don haka ban hada da su a cikin lissafin ba, har sun samu aikin yi, don a maganar tallafin har da samar da aikin yi, don haka ko da wannan Cuta ta Cobid-19 ta zo sai muka ga me za mu yi don bada tallafi ga jama’a. Don haka, farko sai muka bayar da horo ga Malaman addini don su fahimci yadda cutar take da kuma irin taimakon da za su bayar, sannan muka kalli masu bada ilimi a unganni irin su Ungozoma muka shigo da su don su wayar da kan jama’a kan yadda wannan Cuta ta Cobid-19 take da kuma hadarin ta, sannan mun raba sabulai da kuma Amawalin fuska don karya daga cutar, kuma mun raba abinci a jihohi da dama tun daga nan Arewa zuwa Kudu saboda ita wannan Gidauniyar ta kasa ce baki daya tana kallon kasar ne duka mun yi shirye shirye a gidajen Rediyo domin wayar da kan jama’a, kai har ma da aka ce za a dawo makaranta a Jami’a mun yi feshi da kuma bayar da abubuwan kariya daga cutar a Jami’ar Bayero ta Kano da sauran makarantu.
Ta bangaren rashin Lafiya ko kuna daukar nauyin masu dauke da wasu cututtuka?
E hakan ta na faruwa domin wasu su kan kawo wasu matsaloli na rashin Lafiya muna yi, to Amma abubuwan sun yi yawa, kullum kana kallon me za ka yi wa mutum wanda shi ma nan gaba zai taimaki jama’a da shi. Kamar bada ilimi don haka mun fi mayar da hankali wajen bayar da ilimi ga mai karatun fannin Lafiya, wanda za su dawo su taimaka wa jama’a, kuma bayar da tallafin da na ke magana ya kama tun daga matakin Digiri na farko har zuwa P H D mu ke bayarwa.
Ita wannan Gidauniyar tallafin ta ya shiga har karkara ne ko ya tsaya ne a cikin birni?
To gaskiya ya hada ko’ina, muna karbar abin ta duk in da ya zo ko a birni ko daga kauye, to Amma a tsarin da mu ke da shi a wannan shekarar za a karfafa wajen zakulo yaran da su ke da basira, wasu ma suna cikin makaranta ne saboda yanayi da kuma maraici abin ya gagara, don haka za mu zakulo irin wannan ta yadda idan mun samu labari mun tabbatar za mu rubuta wa ita makarantar bukatar mu ta daukar nauyin irin wadannan dalibai. Amma dai abu muhimmi da mu ke kallo, shi ne mu ga duk wanda za mu tallafawa din ya zama yana bukatar hakan. Har ma abn da ya shafi tsro muna bada tallafi, domin ita wannan Gidauniyar tana so ne ta canza daga irin abin da aka saba da shi a baya wajen bayar da tallafi, don haka mu ke yin amfani da bayanai na gaskiya, don haka ko a fannin kasuwanci mun hada kai da wata cibiya mun horas da Matasa yadda harkokin kasuwanci su ke na zamani musamman a yanar gizo kuma mutane wajen 600 ne suka samu horo a kan harkar kasuwancin wanda za su iya yin amfani da shi ko a Facebook ma kadai domin su dogara da kan su. To gaskiya abubuwan da Gidauniyar ta ke yi suna da yawa. Ko a bangaren marayu ma da ba su da abinci Idan aka bincika aka ana ba su. To akwai dai sauran tsare tsare da mu ke da su wanda har yanzu ba mu fitar ba, sai mun samu amincewar Shugaban tafiyar za mu fita. In da za mu duba mu kuma fadada a kan abin da ya shafi hakkin dan Adam, don ko a kwanakinnan mun shiga irin wannan wajen kubutar da wani da aka daure saboda wasu kudade wanda mutumin yana da iyalan da mutunci to wannan Gidauniyar ta tsaya an fitar da shi daga ciki aka biya kudin. Sannan muna kokaki mu ga harkar nan ta fyade an samu saukin ta ta hanyar wayar da kan jama’a da kuma tsaya wa wadanda aka zalunta.
A cikin wannan aikin na ku na taimakon al’umma ko wanne irin matsalolin ku ke fuskanta?
To gaskiya matsalar ita ce sai ka ga wasu sun zo don a tallafa musu, amma da ka je sai ka ga su ma za su iya tallafawa masu bukata, kuma za ka ga waje ne mai nisa sai an Sha wahala kafin a je, to gaskiya wannan yana cikin matsala da mu ke samu. Matsala ta biyu kuma duk abin da ka yi kana so ka san irin nasarar da aka samu, to wasu sai ka ga ba mu cika samun bayanai daga wajen su ba idan sun warke. Wasu kuma sai ka ga ana tsaka da yi musu magani kamar bangaren Masu Sikila, sai ka ga Allah ya karbi ran su, to wannan yana da matukar Sosa rai. Akwai dai matsaloli masu yawa da mu ke samu saboda abubuwan suna da yawa, sai dai da ya ke al’amari ne na hidima ga jama’a ba za ka nuna gazawa ba, domin abu ne ka ke yi domin Allah don haka da mu da mu ke tafiyar da abin da shi Wanda ya dauki nauyin tafiyar da abin da kudin sa wato Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, duk muna yi ne domin neman Lada, fatan mu dai Allah ya shige mana gaba a kan lamuran mu.
To madalla mun gode.
Nima nagode sosai.