An Yaba Da Kokarin Gwamnan Jihar Yobe Kan Bunkasa Rayuwar Al’umma

Yabo da allasan barka sai kara fitowa suke yi a kan irin salon mulkin da Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni yake shifidawa musamman hobbasarsa a kan abin da ya shafi bunkasa rayuwar al’ummar jihar a cikin kwanaki 100 na farko na zangon mulkinsa, yabo na baya baya nan ya fito ne daga bakin wani matashin dan siyasa a jihar, Alhaji Muhammad Ali Tanumi a tataunawar da ya yi da wakilin Leadership A Yau Lahadi kwanakin baya.

Alhaji Muhammadu Ali Tanimu ya kuma lura da cewa, Gwamna Mala Buni ya cirri tuta a tsare tsaren da ya fito da su don tabbatar da an samu cikakken tsaro a sassan jihar tare kuma kula da jin dadin ‘yan gudun hijira a sassan jihar ta hanyar samar musu da ababen more rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hira da suke a fadin jihar, haka kuma Gwmanan ya tabbatar da jami’an tsaron da suke aiki a jihar suna samun dukkan goyon bayan da suke bukata don sauke nauyin aikinsu na samar wa da a’luummar jihar tsaron da ya kamata.

Haka kuma gwamnan ya samar da gidaje fiye 3600 a wasu manyan garuruwan dake a cikin jihar irinsu Damaturu da Potiskum da sauran garuruwa dake mazabun majalisar dattijai na jihar, ya yi hakan ne don ya saukaka wa al’ummar jihar matsalar gidaje da ta addabi ma’aikata a jihar, wannan wani lamari ne aka kasa samarwa a tsawon shekarun da suka wuce,’ Wannan kokari ne mai matukar mahimmanci, muna kuma alfahari da irin wannnan kokari’ inji Muhammadu Tanimu.

Daga nan ya kuma jinjina ga Gwamnna a kan yadda ya zakulo matashi kuma haziki ya nada a matsayin shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, wato Dakta Muhammadu Goje, wannan yabo ya zama dole ne saboda ganin yadda ‘yan gudun hijira da wadanda ibti’lain ambaliyar ruwa ta shafa suke samun tallafi, ya kuma yaba wa shirin gwamnantin jihar na bayar da magani kyauta ga ‘yan asalin jihar da suke fama da cutar koda, hakan ya kawo sauki ga masu fama da wannnan cutar musamman ganin irin yadda tsadar da jinyar cutar keda shi.

Alhaji Muhammadu Ali Tanimu ya kuma bukaci al’ummar jihar Yobe da su kara hakuri a kan yadda harkar gwamnanti ke tafiya su kuma bayar da goyon bayansu don bunkasa jihar ”Da sannu a hankali dukkan sassan jihar zai amfana da ayyukan alhairi da Gwamnan Mai Mala Buni ya tanada’ inji shi.

Ya kuma yi kira na musamman ga ‘yan asalin jihar dake fafutukar rayuwa a wasu sassan kasar nan da su hada hannu da gwamnan tare da kawo gudunmawarsu don bunkasa jihar, “Don bamu da wani jihar da ta fi jihar Yobe a wajenmu, kuma ga shi mun samu Gwamnan mai kishin jiha da al’ummarmu’ inji shi.

Daga karshe, Muhammad Ali Tanimu ya yi addu’ar Allah ya yi wa Gwamna Mai Mala Buni jagoranci ya kuma kara masa basirar gudanar da mulkn jihar cikin nasara.

Exit mobile version