Daga Bala Kukkuru Legas
Wani matashin dan siyasa a jihar Katsina kuma jigo ajam’iyyar APC mai suna Alhaji Idiris Danliman Funtuwa ya bayyana cewa, Gwamnan jihar Katsina na iyakar kokarin ta a wajen shawo kan matsalar tsaro a duk fadin jihar ta Katsina gaba daya, Danliman ya yi wannan tsokaci ne a garin Funtuwa jim kadan bayan kammala taron addu’ar daurin auren diyar wani dan siyasa mai suna Alhaji Balan maigidan sa dake bangaren ta Saulawa Funtuwa, Idiris Danliman ya cigaba da cewa, a halin yanzu Gwamnatin ta jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari Dallatun Katsina tana cigaba da daukar matakai na kawo karshen ta addanci da garkuwa da mutane da sauran maka man tansu ya kara da cewa babu shakka ansani cewar manoma na karkara da masu hannu da shuni na lunguna da sauran talakawa mazauna wadansu shiyoyi acikin jihar Katsina suna fama da fargaba na zuwan ‘yan ta’adda a muhallan da suke zaune a cikin jihar ta Katsina, ya ce, akan haka yake shawartar al’ummar jihar ta Katsina da su cigaba da yin hakuri da abun da yake faruwa na rashin jin dadi kuma su cigaba da gudanar da adduo’i na musamman domin samun saukin wannan al’amari kuma Idan Allah ya yarda nan bada dadewa ba Allah zai kawo saukin wannan al’amari Inji shi, da fatan Allah ubangiji ya cigaba da zaunar da kasarmu Nijeriya lafiya baki daya sannan kuma na rashin dan siyasar na garin Funtuwa ya cigaba da shawartar matasa ‘yan uwansa na jihar Katsina dana sauran jihohin kasar nan da su kara kaimi a wajen neman ilimi tare da koyan sanao’in hannu domin kaucema fadawa a cikin halin kaka-mukayi a cewar sa da fatan matasan za su dauki wannan shawartar tashi. A karshe ya ce, yana yi wa abokinsa dan siyasa fatan Alheri na samun sukunin gudanar da addu’ar daurin auren diyarsa tare da angonta da fatan Allah ya cigaba da zaunar da su lafiya da Nijeriya baki daya.