Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

An Yaba Da Kokarin Shugaban Karamar Hukumar Yusufari  

by
7 months ago
in RAHOTANNI
2 min read
Yusufari
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Muhammad Maitela,

Al’ummar karamar hukumar Yusufari a Jihar Yobe sun yaba wa shugaban karamar hukumar, Hon. Alhaji Waziri Ibrahim bisa ayyukan ci gaban jama’a wadanda suka hada da tallafa wa masu karamin karfi kayan abinci, samar da magunguna kyauta a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya, domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta da makamantan su.

 

Labarai Masu Nasaba

Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kisan Deborah: Zanga-zanga Ta Barke A Sokoto

Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kisan Deborah: Zanga-zanga Ta Barke A Sokoto

Al’ummar sun yaba wa Hon. Alhaji Waziri dangabe da matakin da ya dauka biyo bayan kiraye-kirayen da ofishinsa ya samu tare da neman aiwatar da irin wadamnan ayyukan ci gaba a karamar hukumar domin farfado da yankin daga matsalolin tsaron da al’ummar jihar su ka sha fama da su na Boko Haram tare da kalubalen rayuwar yau da kullum.

 

Mallam Nasiru Muhammad yana daya daga cikin mazauna garin Yusufari, ya shaida wa wakilinmu cewa karamar hukumar ta taimaka wa talakawa da shinkafa buhu 500 (50kgs), manyan buhunan gero 500 (100kgs) tare da galon na man girki 400. Haka kuma sun yaba da yadda raba kayan ya gudana cikin tsanaki wanda ya shiga lungu da sakon karamar hukumar Yusufari.

 

A hannu guda kuma ya kara da cewa, “Dangane da wannan, za mu yi amfani da wannan dama wajen mika godiya tare da yaba wa kokarin shugaban karamar hukumar Yusufari, Hon. Waziri Kumagannam bisa wannan tallafi na kayan abinci da sauran muhimman ayyukan da yake aiwatar wa, wanda ko shakka babu jama’a sun yi matukar farin ciki da godiya.”

 

A nasa bangaren, Alhaji Mahmud Bamallum Kumagannam ya yaba ne dangane da bai wa sashen kiwon lafiya muhimmanci da shugaban karamar hukumar ya yi, ta hanyar samar da ingantattun magunguna da aka raba a dakunan shan magani kyauta, wanda ya ce hakan zai taimaki masu karamin karfi a irin wannan lokaci wanda zazzabin maleriya da makamantan sa ke addabar jama’a, musamman kananan yara da mata masu juna biyu a karamar hukumar.

 

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Abubuwan Da Suka Karfafa Ni Wajen Tallafa Wa al’umma – Saratu Gidado (Daso)

Next Post

Ko Tsarin Shugabanci Na Firaminista Zai Iya Warware Mishkilolin Nijeriya?

Labarai Masu Nasaba

Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kisan Deborah: Zanga-zanga Ta Barke A Sokoto

Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kisan Deborah: Zanga-zanga Ta Barke A Sokoto

by Abba Ibrahim Wada
2 days ago
0

...

Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kisan Deborah: Zanga-zanga Ta Barke A Sokoto

Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kisan Deborah: Zanga-zanga Ta Barke A Sokoto

by Abba Ibrahim Wada
2 days ago
0

...

Za A Murkushe Ta’addanci A Nijeriya Kafin Karshen 2023 – Sojoji

Za A Murkushe Ta’addanci A Nijeriya Kafin Karshen 2023 – Sojoji

by Sabo Ahmad
3 days ago
0

...

Wajibi Ne Jam’iyyu Su Kiyaye Wa’adin Zabubbukan Fitar Da Gwani -INEC

INEC Ta Soki Masu Neman Shugabanta Ya Fito Takara

by Musa Danmahawayi
7 days ago
0

...

Next Post
Shugabanci

Ko Tsarin Shugabanci Na Firaminista Zai Iya Warware Mishkilolin Nijeriya?

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: