An Yaba Da Kokarin Shugaban Karamar Hukumar Yusufari  

Yusufari

Daga Muhammad Maitela,

Al’ummar karamar hukumar Yusufari a Jihar Yobe sun yaba wa shugaban karamar hukumar, Hon. Alhaji Waziri Ibrahim bisa ayyukan ci gaban jama’a wadanda suka hada da tallafa wa masu karamin karfi kayan abinci, samar da magunguna kyauta a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya, domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta da makamantan su.

 

Al’ummar sun yaba wa Hon. Alhaji Waziri dangabe da matakin da ya dauka biyo bayan kiraye-kirayen da ofishinsa ya samu tare da neman aiwatar da irin wadamnan ayyukan ci gaba a karamar hukumar domin farfado da yankin daga matsalolin tsaron da al’ummar jihar su ka sha fama da su na Boko Haram tare da kalubalen rayuwar yau da kullum.

 

Mallam Nasiru Muhammad yana daya daga cikin mazauna garin Yusufari, ya shaida wa wakilinmu cewa karamar hukumar ta taimaka wa talakawa da shinkafa buhu 500 (50kgs), manyan buhunan gero 500 (100kgs) tare da galon na man girki 400. Haka kuma sun yaba da yadda raba kayan ya gudana cikin tsanaki wanda ya shiga lungu da sakon karamar hukumar Yusufari.

 

A hannu guda kuma ya kara da cewa, “Dangane da wannan, za mu yi amfani da wannan dama wajen mika godiya tare da yaba wa kokarin shugaban karamar hukumar Yusufari, Hon. Waziri Kumagannam bisa wannan tallafi na kayan abinci da sauran muhimman ayyukan da yake aiwatar wa, wanda ko shakka babu jama’a sun yi matukar farin ciki da godiya.”

 

A nasa bangaren, Alhaji Mahmud Bamallum Kumagannam ya yaba ne dangane da bai wa sashen kiwon lafiya muhimmanci da shugaban karamar hukumar ya yi, ta hanyar samar da ingantattun magunguna da aka raba a dakunan shan magani kyauta, wanda ya ce hakan zai taimaki masu karamin karfi a irin wannan lokaci wanda zazzabin maleriya da makamantan sa ke addabar jama’a, musamman kananan yara da mata masu juna biyu a karamar hukumar.

 

 

Exit mobile version