An yaba ma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, yabon ya fito ne daga bakin Birgediya Janar Maharazu Isma’il Tsiga mai ritaya Basarake, manomi, dan siyasa shi ne Barden Kudun Katsina a fadarshi dake garin Tsiga a karamar hukumar Bakori dake jihar Katsina.
Barden Kudun Katsina ya yi hira da manema labarai a makon da ya gabata jim kadan da kada kuri’arshi a zaben cike gurbi na dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Bakori a majalisar dokoki ta jihar Katsina a sanadiyyar rasuwar dan majalisar jihar.
Birgediya janar ya cigaba da cewar babu shakka ya gamsu kwarai akan yadda yaga shirin hukumar zaben yadda suka samar da kayan zabe gamsassu da kai kayan zabe cikin lokaci da bude rumfunan zabe cikin lokaci da na’urar tantance masu jefa kuri’a, wannan ya nuna hukumar zabe ba irin wadda aka sani a shekarun baya bace domin duk abinda masu jefa kuri’a suke nema wadda doka ta tanadar hukumar zabe ta kawo kuma babu shakka mutane sun fito wajen zaben kuma anyi zabe lafiya domin babu inda aka sami tashin hankali ko wani yamutsi.
Daganan yayi kira ga masu jefa kuri’a su kara rike ‘yancin su domin kuria ce yancin su, kuma su ma al’umma sun fara ganewa domin sun san kuriar itace yancin su.
Alhaji Maharazu Tsiga wanda ya taba neman kujerar dan majalisar dattawa a mazabar shiyyar Funtuwa a jam’iyyar APC wanda ya kara kira ga duk wanda bai samu nasara ba da yayi hakuri domin mulki na Allah ne shi ke badawa kuma komai lokaci gareshi don haka don Allah wanda duk ya samu nasara ya gode ma Allah kuma wanda ya samu kada ya dauka kamar ya fi kowa ne, shi kuma wanda bai samu ba kada ya dauka ko Allah baya sonshi ne, wannan ba haka bane, yace yanzu ina wanda ya fara cin zaben Allah yayi mashi rasuwa da fatan Allah ya jikanshi, Barden kudun Katsina yace duk dan siyasar dake son ya koyi hakuri yazo wurinshi don yasan komai na Allah ne.
Shi dai Alhaji Maharazu Tsiga yana na farko farkon da ya fito neman kujerar sanatan yankin Funtuwa a Jam’iyyar APC amma bai samu ba kuma yayi hakuri inda yake zaune a garinsu cikin Al’ummarshi inda yake taimakon jama’ar yankin su, wakilinmu ya gano yadda jama’ar garin ke yaba mashi da yayi ritayar aikin soja ya dawo gida yake taimakon Al’umma a lokaicn da yake aikin soja ya taimaki matasan yankin da samun ayyukan gwamnatin tarayya da samar ma matasan yankin da sauran Al’umma tallafi daban daban.