Ibrahim Muhammad" />

An Yaba Wa Ayyukan Da Ganduje Ya Yi A Kano

An bayyana nasarar da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samu a karo na biyu da cewa tana da nasaba da irin dinbin ayyukan alkhairi na ci gaban jihar Kano da ya yi a fannoni da dama. Shugaban daya daga cikin kungiyoyi da sukayi gwagawarmayar ganin nasarar Ganduje da ake kira da “Ganduje House to House Campaign” Wato masu tallata manufofin Ganduje Gida-gida, Abba Usman Alto ya bayyana haka.

Ya ce, Gwamna ya yi ayyuka na ci gaban kasa ta inganta harkar sufuri da inganta ci gaba da bunkasar noma a jihar Kano da harkar ilimi da kuma gina matasa akan fannoni da daman a aikin yi da dogaro da kai.

Abba Usman Alto ya yi nuni da cewa wananan nasara da Gwamna ya samu wani karin damane da zai ci gaba da gudanar da ayyuka daya somo shi yasa ma a matsayinsu na matasa masu son ci gaban Kano suka tsaya suka nunawa al’ummar Kano muhimmancin sake zabar Gwamna dan ya dawo karo na biyu ta bin gida-gida kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ya Shawarci Gwamna Ganduje da cewa a wannan karo ya kamata ya fadada dama da yake baiwa matasa a cikin tafiyar mulkinsa duba da irin rawar da suka taka kuma sun yi farin ciki da alakawari da ya yi ranar rantsuwa na cewa zai samar da ma’aikata mai zaman kanta ta matasa wannan inya tabbata zai bunkasa ci gaban matasa sosai.

Abba Usman Alto ya yi kira ga al’ummar Kano a kan su taho a marawa Gwamna Ganduje duk wanda kuma yake gani anyi masa abinda ba daidai ba ya yi hakuri yazo a dafawa wannan Gwamnati asa Kano a gaba duba da cewa Gwamna da kansa ya furta Kalmar yin yafiya ga duk wani wanda ya bata masa. Kuma Gwamna Ganduje duk wani abu da aka ga ya yi a Kano manuface ta kawao ci gaba da bunkasarta. Ganduje ya samu a karo na biyu da cewa tana da nasaba da irin dinbin ayyukan alkhairi na ci gaban jihar Kano da ya yi a fannoni da dama.

Exit mobile version