Muhammad Awwal Umar" />

An Yaba Wa Gwamnan Neja Kan Nada Nma Kolo Mashawarcinsa Na Siyasa

An yaba wa gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello kan zaben nagartattun mutane a matsayin wadanda za su kula da sauke nauyin gwamnati kan muradun ciyar da Neja gaba.

Jigo a jam’iyyar APC kuma shugaban yakin neman zaben Sanata Sani Musa 313, Alhaji Hamza Yanga Buba, ne ya yi wannan yabon a Minna, babban birnin jihar ta Neja.

Dattijon ya ce zaben Alhaji Yakubu Sallau a matsayin janar manaja na hukumar kula da sufurin motocin gwamnati abin a yaba ne, domin Alhaji Yakubu Sallau, ya shugabanci karamar hukumar Chanchaga tsawon shekaru takwas kowa ya ga irin rawar da ya taka na ciyar da karamar hukumar gaba, bayan nan ya jagoranci hukumar kula da kungiyoyi masu zaman kansu wanda ya taimaka wajen hada kan kungiyoyi dan samun nasarar zaben jam’iyyar APC a babban zaben da ya gabata, wanda a tarihin jihar nan ba a taba samun hadin kan kungiyoyi ba wajen marawa gwamnati baya kuma har aka samu nasarar amincewar jama’a, wanda hakan ya sa jihar nan ta zamo sahun gaba wajen yin zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu hatsaniya ba.

Da ya juya kan mukamin mai baiwa gwamnati a kan harkokin siyasa kuwa ya ce hakan ya yi daidai, domin Hon. Muhammad Nma Kolo mutum ne mai kishin jihar da ya taka rawar gani wajen horar da daruruwan jama’a sana’o’in hannu wanda yanzu haka da daman jama’a na cin moriyar wannan shirin.

Yace Hon. Nma Kolo mutum ne da yasan siyasa kuma ya taka rawar gani tun farkon siyasar 1999 wanda ya taimaki gwamnati wajen samun nasara a fannoni da dama, dan haka irin rawar da ya taka wajen samun nasarar sanata mai kula da wannan yankin tun daga kan zabe har zaman kotu da kuma irin taimakawa gwamnati a wasu matsalolin da suka rika tasowa a baya, ta fuskar shawarwari da kuma ganin an shawo kan matsalolin ya cancanci wannan matsayin.

Dan haka dattijon ya jawo hankalin gwamnatin jiha da ta kara jajirce wa a sauran mukaman da suka rage wajen ganin an jawo mutane masu akida da sanin ya kamata daga dukkanin bangarorin jihar nan dan samun nasarar sauke nauyin da ke kan ta.

Yace duk masu korafi su jure domin ba mukami ne abin bukata ba, yin aiki tukuru da zai daga jihar gaba itace manufar jam’iyyar APC, a bangaren mu dukkan wanda gwamnati ta tabbatar zai rike amana da yin aiki tukuru a shirye muke da mu bi shi.

Exit mobile version