Daga Abubakar Abba,
An yaba wa kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke kan yi na samar da cibiyoyi hudu na warkar da masu tu’amalli da kayan maye a jihar.
Yabon ya fito ne daga bakin Shugabar Gidauniyar tallafa wa Mata da Matasa da ake kira a turance Eye Opener Women & Youth Foundation, Uwargida Magret Juliu.
Uwargida Magret Juliu ta kuma yi nuni da cewa, , Cibiyoyin za su taimaka matuka wajen dai daita rayuwar su da kuma samar masu da lafiya.
Shugabar Magret Julius ta sanar da hakan ne a kaduna a hirar ta kamfanin dillancin labarai na kasa, inda ta yi nuni da cewa, lamarin abin damuwa ne matuka.
Magret Julius ta yi nuni da cewa, lamarin abin damuwa ne matuka.Ta kuma koka kan yadda wasu mata da matasa ke yin tu’amalli da kayan maye.
A cewar Uwargida Magret Julius, tsamo matan da matasan da suka cusa kansu a cikin harka ta shan kayan maye, abu ne da ke bukatar sa hannun ‘yan uwa da kuma alummar gari.
Shugabar Uwargida Magret Julius ta ci gaba da cewa, “Gidauniyar mu na kan gudanar da aiki kafada da kafada da ‘yan uwan irin wadanan masu yin tu’amalli da kayan maye kan yadda za a tsamo su daga cikin mummnar dabi’ar, inda ta yi nuni da cewa, akwai kuma bukatar ‘yan uwan masu yin irin wannan dabi’ar su dinga nuna maau so da kauna ba tare da nuna masu kyama ba”.
Uwargida Magret Julius ta kara da cewa, “ Gidauniyar na bayar da shawara da kuma janyo ‘yan uwa da shugabannin alumma da kuma masu ruwa da tsaki domin wayar da kai kan yadda za su kula da irin wadannan masu dabi’ar da suka tsuduma a cikin matsala sanadiyyar yin tu’amalli da kayan maye.
Ta kara da cewa , “Idan matsalar ta kama mutum daya, kamar ta shafi daukacin ‘yan uwa ne da kuma daukacin alumma, inda ta bayyana cewa, hakan ne ya sa muka zage tukuru, wajen yin fadakar wa kan illolin dake tattare da yin tu’amalli da kayan maye da kuma irin matsalar da dabi’ar ke haifar wa masu yin ta.
Ta ce, Gidauniyar ta kuma gudanar da tarurtuka da ban da ban kan yadda ‘yan uwa za su taimaka wa masu tu’amalli da kayan maye da suka samu wasu larurori domin su samu sauki su kuma koma cikin alummma su ci gaba da rayuwa ta gari.
Uwargida Magret Julius ta yaba wa Gwamatin Tarayya da kuma Gwamnatin jihar Kaduna kan kokarin da suke ci gaba da yi na yakar shan kayan maye.
Ta karada cewa, Gidauniyar ta yi hadaka da Hukumar yaki da sha da safafar kayan maye NDLEA da kuma Hukumar yaki da sha kayan maye mallakar gwamnatin jihar KSBDSA domin tabbatar da Yaki da shan kayan maye a daukacin fadin jihar.
Uwargida Magret Julius, Gidauniyar na kuma dora mutane kan yadda za su koyi sana’oin hannu, musamamn a tsakanin mata da matasa, inda ta kara da cewa , Gidauniyar ta kuma horar da sama da mata da matasa 1,000 kan sana’oin hannu da ban da ban da suka hada da yin Takalma, Jakankuna, aikin Tela da sauransu.
Uwargida Magret Julius ta sanar da cewa, horon an bayar dashi ne ta hanyar sauran kungiyoyi masu ra’ayi daya kuma Gidauniyar ta rabar da kyautar ‘ykn kudade ga wadanda suka amfana da horon domin su fara gudanar da kasuwanci don su zamo masu dogaro da kawunan su, inda ta yi kira ga matasa da su yi watsi da yin tu’ammali da kayan maye, musamamn domin kare lafiyarsu da kuma ganin cewa, sune manyan gobe.