Connect with us

RIGAR 'YANCI

An Yaba Wa Sanata Sabi Kan Ayyukan Raya kasa Ga Yankinsa

Published

on

An yabawa sanata mai wakiltar Neja ta arewa, Sanata Aliyu Sabi kan yunkurinsa na kammala ayyukan hanya a yankunan kananan hukumomin da yake wakiltar a majalisar dattijai ta kasa. Sarkin bakin Kontagora, Alhaji Abubakar dan Usman ne yayi yabon a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a Kontagora, littinin din makon nan.

Sarkin bakin ya cigaba da cewar duk da halin da tattalin arzikin kasar nan ke fuskanta, dan majalisar bai yi kasa a guiwa ba wajen gabatar da kudurce kudurcen da zasu anfanin jama’a. Yace ko a zangon farko na wakilcin dan majalisar dattijan ya samo ayyukan daga gwamnatin tarayya wanda yanzu ake cin anfanin su, misalin daya daga cikin irin wadannan ayyukan shi ne aikin hanyar Kontagora zuwa Yauri da iyaka da jihar Kebbi wanda tuni an kammala shi kuma ana anfani da wannan hanyar a halin yanzu wanda tana daya daga cikin hanyoyin da jihar nan ke anfana da shi mallakin gwamnatin tarayya. Yanzu haka akwai aikin hanya cikin karamar hukumar Kontagora da Rijau da wasu kananan hukumomi da ake kan aikin su.
A wannan gabar za mu ce ba mu yi zaben tumun dare ba, ina da tabbacin yadda maigirma Sanata Aliyu Sabi Abdullahi yake da burin samar da abubuwan cigaba a yankin nan da yake wakilta daga gwamnatin tarayya, idan jama’a suka kara hakuri suka baiwa gwamnati goyon baya bisa jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, yankin Neja ta arewa za tafi kowa anfana da wannan mulki na shekaru takwas a inuwar APC.
Sarkin bakin ya ce, za mu cigaba da wayar da kan jama’a wajen baiwa gwamnatin da suka zaba da kuri’arsu goyon baya dan samar da romon mulkin dimukuradiyya a yankin nan.
Sarkin bakin ya jawo hankalin matasa da su rungumi harkar noma musamman dan ganin an samar da ayyuka ga jama’a domin kuduri ne gwamnati na samar da abinci da dawo da martabar noma a yankin Neja ta arewa, dan ganin bangaren noma na taka rawar ganin wajen bai wa jama’a aiki da daga martabar kasar nan ta hanyar samun kudaden shiga ga gwamnati ta yadda za ta samu kwarin guiwar cigaba da ayyukan raya kasa da ta sanya a gaba.
Alhaji Abubakar dan Usman, ya jawo hankalin dan majalisar dattijan da ya kara da ya kara taka rawar gani wajen gabatar da kudurce-kudurcen da talakawa za su amfana ga majalisar dattijai, don gabatar da dokokin da zasu cigaba da taka rawar ganin wajen bunkasa tattalin arzikin yankin nan.
dan Usman ya nemi jama’a da su cire bambamce bambamcen siyasa wajen cigaba da goyawa gwamnatin baya, don samun nasarar kammala ayyukan cigaban kasa da ta sanya a gaba.
Yace matsalolin da a ke fuskanta a yanzu, matsaloli ne da in jama’a su ka bai wa gwamnati goyon baya da addu’o’i za a iya kawo karshen da taimakon Allah, yanzu kowa na ji a jikinsa kuma dole kowa ya bada gudunmawarsa wajen ganin an karfafa gwiwar gwamnati wajen lalubo hanyar da za a magance su.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: