Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko
An bayyana matakin amince wa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na samar da sabon albashi na musamman ga malaman makarant a, da cewar batu da duk wani malami da kuma mai kishin ilimi da ke Nijeriya.
Shugaban kungiyar malaman makaranta ta Nijeriya reshen karamar hukumar Zariya, Kwamared Abdulhamid D.Adamu ya bayyana wannan yabo, a lokacin da ya zanta da wakilimu da ke Zariya.
Kwamared Abdulhamid Adamu ya ci gaba da cewar, wannan batu na neman gwamnatin tarayyar Nijeriya ta samar da sabon tsarin albashi na bai-daya ga malaman makaranta a Nijeriya an kwashe shekara fiye da ashirin shugabannin kungiyar malamai ta Nijeriya das ka gabata su na neman shugabannin baya su amince a samar da tsarin albashin, amma, al’amarin ya ci tura, a cewarsa, sai a wannan shekara shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da wannan bukata na malaman Nijeriya.
Kwamared Abdulhamid ya kuma ce, yanzu malaman makaranta a Nijeriya za su yi gogayya da sauran malamai a sassan duniya, tun da sun sami matsayin da sauran malaman sassan duniya suka samu, day a zama silar yadda su ke zage damtse, wajen koyar da yaran al’umma da kuma kula da tarbiyyarsu bakidaya.
Duk da matakin da shugaban kasa ya dauka na na ganin ya share wa malamai hawaye, Kwamared Abdulhamid Adamu ya jinjina wa gwamnan jihar Kaduna na yadda ya kara albashi ga ma’aikatan jihar Kaduna baki daya, wannan ma, a cewarsa, duk wani malami da ke jihar Kaduna, ya sami canijn rayuwa day a samu na motsin da gwamnan jihar Kaduna ya yi.
A kuma tsokacin da shugaban kungiyar malaman makaranta ya yi na yadda gwamnatin tarayya ta amince da karin shekara biyar ga malaman makaranta na ritayarsu, maimakon malami ya yi ritaya a shekara a lokacin da ya cika shekara talatin da biyar ya na koyarwa ko kuma ya na aiki a ma’aikatar ilimi, wannan, kamar yada y ace, zai kara wa malami zummar ci gaba da bayar da gudunmuwarsa, wajen ciyar ilimi gaba da kuma kula da tarbiyyar daliban da aka danka ma sa.
Ya kuma jinjina wa shugaban karamar hukumar Sabon gari Injina Mohammed Usman, na yadda ya lashi takobin fara biyan malaman firamare hakkokinsu na karin girma da aka dade da yi ma su a takarda, amma batun karin kudi a cikin albashinsu ya ci tura a shekarun da su ka gabata.
Kwamred Abdulhamid Adamu ya lashi takobin ba shugaban karamar hukumar duk goyon baya da shawarwarin da suka dace, domin ya sami damar aiwatar da wannan muhimmin al’amari da ya sa wa gaba, na ciyar da malamai gaba da kuma kulawar day a ke yi wa sashin ilimi a karamar hukumar Sabon gari baki daya.
A karshe, Kwamred Abdulhamid D. Adamu ya jawo hankalin daukacin malaman makaranta da suke Nijeriya musamman wadanda su ke karamar hukumar Sabon gari da su kara tashi tsaye, wajen koyarwa da kula da tarbiyyar daliban da aka danka ma su.