An yankewa wasu ma’aurata, Ebiesuwa Abayomi Fredrick da matarsa, Tinuola Idayat Oyegunle, hukuncin daurin shekaru 40 a kan gidan yari kan damfara ta Naira milayan 53.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya da ke zaune a garin Ibadan na jihar Oyo, a 15 ga watan Fabrairun 2021 ta same su da laifi a dukkanin tuhuma hudu da ake yi musu, na hada baki da kuma samun kudi ta hanyar bogi da karya ga ofishin shiyya na shiyyar Ibadan na hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zangon kasa.
Ma’auratan, a cikin wani tsari na damfarar kudi na gaba, sun gudu da kudi wata mai suna, Dunni Olateru Olagbegi na Naira miliyan 53,713,260.00, a tsabar kudi da kuma banki inda suka yi amfani da hanyar ruhaniya da tsafi don kauce wa mutuwar ba zata, inda suka dauki jakar Ghana-Must-Go wacce aka cika ta da takardar kudin Dalar Amurka a cikin but din mota.
Wacce abin ya shafa ta taba shiga motar haya tare da wasu fasinjoji uku a watan Mayun 2013, wadanda ba ta san su ba, wanda suka kasance mambobin kungiyar ‘yan damfara ne. Ta na shiga motar, sai ta ji wasu fasinjoji uku da suka magana akan wata jakar Ghana-Must-Go da ke cike da Dalar Amurka a cikin but din motar.
A yayin gudanar da bincike, An gano cewa an biya sama da Naira Miliyan tara ga wanda ake kara na biyu, a asusun Tinuola Idayat Oyegunle a daya daga cikin bankunan na uku, baya ga wasu kudade da aka gano ga wanda ake kara na farko, asusun Ebiesuwa Abayomi Fredrick.
An kuma gano cewa wanda ake tuhuma na farko ya gina wani otel na ‘Bictoria East Park Hotel & Suite’ da ke Igbogbo, Ikorodu, Jihar Legas daga cikin kudin.
A hukuncin da ya yanke a ranar, mai shari’a Abdulmalik ya samu ma’auratan da aikata laifuka hudu kuma ya yanke hukuncin daurin shekaru 10 a kan kowannensu daga tuhume-tuhumen hudu. haka zalika, yayin da wa’adin gidan yarin Ebiesuwa zai fara aiki daga 19 ga Yuni, 2017 lokacin da aka kama shi, lokacin Tinuola a cikin ‘Custodial Center’ zai fara kirgawa daga 26 ga Mayu, 2017 lokacin da aka kama ta.
Alkalin ya kuma bayar da umarnin cewa a sayar da otel din na ‘Bictoria East Park Hotel & Suite’, a ci gaba da shari’a, idan ba zai kai Naira Miliyan 53,713,260.00 ba, a biyan wacce aabin ya shafa sauran kudin ta a cikin asusun Gwamnatin tarayya.”