Babbar kotun sojoji ta 7 da ke zaune a Maiduguri ta yanke wa wani sojan ruwa, Pte. Azunna Mmadu-Abuchi hukuncin kisa ta hanyar harbi har sai ya mutu, saboda kama shi da laifin kashe wani jami’i, Laftanar Babakaka Ngorgi.
Da yake yanke hukunci a jiya, Shugaban Kotun, Birgediya Janar Arikpo Ekubi, ya ce mai gabatar da kara ya tabbatar da kararsa ba tare da wata tantama ba cewa wanda ake zargin ya harbe shi da gangan har ya kashe Ngorgi, wanda shi ne mai jagorantar Bataliya ta 212, Bama.
“Da gangan kuka bude wuta kuka wofintar da mujallarku ta alburusai tara a kan jami’in da ya mutu, Laftanar B.S Ngorgi, wanda shi ne Adjutant na Bataliya ta 212, Bama, wanda ya yi sanadin mutuwarsa nan take. “Kun ci amana da amanar da Sojojin Najeriya suka ba ku don tabbatar da mutunci da girmama rayuwar dan adam.
“Don haka ana kallon abin da ka aikata ba abu ne na jin dadi ba, da kuma cin fuska ne ga kokarin da shugabanin sojojin na yanzu ke yi wanda ke jaddada kare hakkin dan’Adam da kwarewa a yayin sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ba ta.
“Duk da haka, girman laifin da ka aikata a kan jami’in mara laifi wanda ta hanyar aikace-aikace, laifi ne ga hakkin bil’Adama da kuma kokarin shafawa kyakkyawan sunan sojojin Nijeriya kashin kaji, dole ne a sanya doka yadda ya kamata. “Babbar kotun sojoji, domin hukunci kan aikata laifin kisan kai kamar yadda sashe na 106 na dokar soja ta tanada shi ne mutuwa. Za a zartar da wannan hukuncin ne ta hanyar harbi, ”in ji shi.
Ekubi ya kuma yankewa wasu sojoji hudu hukunci saboda an same su da hannu a azabtar da farar hula daya mai suna Peter Apogu, har lahira kan batan batirin mota. Dangane da yanayin shigar su cikin aikin, Saja Sani Ishaya wanda shi ne shugaban tawagar an yanke masa hukuncin shekara hudu a gidan yari, Lance Cpl. Fabiyi Bidemi zai yi shekara biyu yayin da Pte. Adamu Abdulrashid da Pte. Musa Bala zai yi shekara daya kowannensu.
Kotun ta kuma yanke wa wani Pte Mohammed Kuru hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari sakamakon harbin bazata a wani bikin farar hula da ya kashe wani yaro dan shekara 12. Daya Lance Cpl. Aja Emmanuel an rage masa mukami saboda cin zarafin wani farar hula wanda hakan ya haifar masa da “mummunar cutar jiki”. Alkalin kotun, duk da haka ya ce dukkan hukunce-hukuncen suna karkashin tabbatarwa ne daga babbar hukumar da ta dace kamar yadda yake a karkashin sashe na 151 karamin sashe na 1b da kuma sashe na 152 karamin sashe na 1b na dokar rundunar sojan.
Da take magana a karshen zaman, Kodinetan Borno na Hukumar Kare Hakkin Dan-Adam ta kasa, Misis Jummai Mshelia, ta yaba wa Sojojin na Nijeriya kan kwarewarsu da kuma nuna girmamawa ga ‘yancin dan’Adam. (NAN)