Connect with us

WASANNI

An Yankewa Marcelo Hukuncin Shekara Biyu A Gidan Kaso

Published

on

Dan wasan Real Madrid Marcelo Bieira ya amince cewa ya zille wa biyan haraji inda ya yarda a yi masa daurin je-ka-ka-gyara-halinka na wata hudu kamar yadda rahotanni suka bayyana daga kasar Sipaniya.

Rahotanni sun ce dan wasan dan kasar Brazil mai shekara 30 ya ha’inci hukumomin Sipajiya $576,000 ta hanyar yin amfani da kamfanonin kasashen waje wurin tafiyar da harkokin kudinsa sai dai zai biya tarar €750,000.

Marcelo dai yana daya daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa da hukumomin karbar haraji suka hukunta saboda rashin biyar haraji yadda yakamata kokuma gujewa biyan gaba daya.

Marcelo ya amince cewa ya kauce wa biyan haraji kuma an rage masa daurin da ya kamata a yi masa ne dama tarar da ya kamata ya biya a wani bangare na yarjejniyar da ya kulla da masu shigar da kara, a cewar rahoton wani rahoto.

Dokokin kasar Sipaniya sun amince wanda ya aikata laifi karon farko ya sha daurin je-ka-ka-gyara-halinka na shekara biyu, don haka ana sa ran ba zai yi zaman gidan yari ba.

An zargi ‘yan wasan kwallo kafa da dama da kauce wa biyan haraji, cikin su har Lionel Messi, Neymar da Cristiano Ronaldo da kuma dan wasa Angel Di Maria wanda yanzu yake buga wasa a PSG.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: