Jiya Lahadi Madarasatul Uthman bn Affan Li tahfizul kur’an da ke garin Argungu ta yaye dalibai saba’in da daya a karo na hudu.
Malam Nasir Abubakar shi ne wanda ya assasa ta kuma har wa yau shi ke rike da ragamar makarantar ya bayyanawa wakilinmu da cewa tun lokacin da aka assasa wannan makarantar shekaru takwas zuwa yau an yaye dalibai dari biyu da talatin da uku (333) wadanda muna kyautata zaton ba mu da haufi ga karatunsu saboda yanzu haka bayan kananan yara yan kasa da shekaru goma akwai wadanda suke hafizan Al’kur’ani ne bayan wadansu karance-karance da ake gabatarwa.
A wannan shekara dai daga cikin daliban da aka yaye sun hada da maza 35 mata kuma 36.
A daya bangaren kuma Malam Nasir ya ce ba za a rasa damuwa ba a cikin kowane al’amari amma dai babbar damuwar wannan makarantar ita ce rashin biyan kudin makaranta ba daga bangaren iyaye wanda wadannan kudaden ne ake hadawa don biyan albashi.
Dokta Zainab matar gwaman jihar Kebbi wacce Amira Nasare shugabar kungiyar mata musulmi reshen jihar Kebbi ta wakilta ta bayarda gudummawar #200,000:00k sannan kuma ta yabawa wannan yankin na masarautar Argungu bisaga gudummawarda su ke bayarwa a bangaren addini.
Haka zalika Honarabul Nasir Dan Umma Danmajalisa mai wakiltar karamar hukumar mulki ta Argungu ya bayarda gudummawar stampa ga dalibai mata da kuma yadi goma-goma ga maza 35, Sarkin Alhazzan Kabi Alhaji Auwalu Danjimma ya yadi 25 da kuma atampa 5, Alhaji Isah Lailaba ya bayarda shadda ga dalibai maza da kuma atampa ga mata, Alhaji Sani Dan Maimiya Babban Manajan Yargiwa Supermarket Argungu ya bayarda gudummawar atampa 71.
Taron walimar dai ya sami halartar shugabannin addini daga ciki da wajen jihar Kebbi da ’yan kasuwa da ’yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati inda iyaye da masoya suka gabatar da kyautuka ga daliban da suka sauke Al’kur’ani mai tsarki.