An Yi Alluran Riga-kafin Covid-19 Fiye Da Biliyan 1 A Kasar Sin

Daga CRI Hausa
A cewar shafin yanar gizo na Hukumar Lafiya ta Kasar Sin, ya zuwa ranar 19 ga watan Yunin shekarar 2021, larduna 31 (yankuna masu cin gashin kansu da biranen dake karkashin ikon babban yankin gwamnatin kasa) da rukunin sojoji ma’aikata masu ba da taimako a jihar Xinjiang sun ba da rahoton cewa, jimilar alluran riga kafin COVID-19 da aka yi sun wuce biliyan 1 a halin yanzu, kasar Sin tana matsayin farko wajen yawan riga-kafin da aka yi da kuma yawan al’ummar da aka yiwa riga-kafin.

A sa’i daya kuma, shirin “spring sprout” na kasar Sin ya kuma yi alluran rigakafin sama da miliyan 1 ga ‘yan kasarta dake kasashen duniya fiye da 150.

Ban da wannan kuma, ba kawai kasar Sin tana ba da muhimmanci ga kiyaye tsaro da lafiyar ‘yan kasar ba ne, har ma tana mayar da hankali sosai kan kiyaye lafiyar ‘yan kasashen waje da ke kasar.

A halin yanzu, yankuna da yawa a cikin kasar Sin sun shigar da ‘yan kasashen waje cikin tsarin shawo kan riga-kafin annobar da tsarin aiki na kananan al’ummomin don ba da tabbaci ga biyan bukatunsu yadda ya kamata.

Aikin bincike da bunkasuwar alluran riga-kafin COVID-19 na kasar Sin yana a mataki na farko a duniya, kuma kasar Sin na tsayawa tsayin daka a sahun farko na hadin gwiwar allurar riga-kafin kasa da kasa. Baya ga haka, kasar ta yi alkawarin samar da alluran riga-kafin a matsayin kayayyakin amfanin jama’a na duniya baki daya. Kana tana ba da tallafin riga-kafin ga kasashe masu tasowa dake da bukata cikin gaggawa da sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasashe daban daban.

Bugu da kari, bayanai daga Ma’aikatar Kasuwanci ta Kasar Sin sun nuna cewa, ya zuwa farkon watan Yuni, kasar Sin ta riga ta fitar da alluran riga-kafin zuwa kasashe sama da 40. Tana kuma taka rawa sosai a cikin shirin “COVAX” na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya zuwa yanzu dai ta riga ta kammala rukunin farko na alluran rigakafin a hukumance. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Exit mobile version