CRI Hausa">

An Yi Allurar Rigakafin Cutar COVID-19 Miliyan 10 A Kasar Sin Ba Tare Da Samun Matsala Ba

Ran 30 ga watan Disamba na shekarar bara, bayan allurar rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar ya samu iznin shiga kasuwa a UAE da Bahrain, yanzu ya samun izinin shiga kasuwar kasar Sin. Kafin wannan kuma, an yi amfani da wannan allura cikin gaggawa a kasar Sin, UAE da Bahrain da Masar da Jordan. Ban da wannan kuma, shugabanni da kusoshin kasashe 10 sun samu wannan allura. Har wa yau, kasashe fiye da 50 suna bukatar sayen wannan allura.
A cikin kasar Sin, an yi wa mutanen da yawansu ya kai miliyan 1 wannan allura a birnin Beijing, inda a birnin Shanghai wannan adadi ya kai dubu 602, yawan allurar da aka yi amfani da su a kasar Sin ya kai fiye da miliyan 10. (Amina Xu)

Exit mobile version