An Yi Artabu Tsakanin Tsageru Da ‘Yan Sanda A Legas

Kayayyakin Da Aka Wawure

Daga Abubakar Abba

 

A jiya Talata, jami’an ‘yan sanda a jihar Legas suka yi artabau da wasu tsagerun matasan Yarabawa da aka fi sani ‘yan Area Boys a yankin Apapa cikin jihar.

 

An ruwaito cewa, artabun a tsakanin tsagerun da jami’an ta auku ne saboda haramtattun ayyukan da suke aikatawa a yankin.

 

Wani ganau, ya shaida wa manema labarai cewa, gammaiyar jami’an tsaro sun dira a qofar farko ta shiga Tin-Can da ke a Mile 2-Apapa a kan babbar hanya  domin cin laggon tsagerun da ake zargi da aikata muggan laifuka a yankin.

Rahotanni sun ce, gamaiyar ta jami’an tsaron, sun hada da, na ‘yan sanda, dakarun soji da kuma na hukumar rage cunkuso ta jihar (LASTMA).

 

An ruwaito cewa, tsagerun ne suka fara yin ruwan Duwatsu da Kwalabe a kan motocin jami’an tsaron a lokacin da suka je yankin domin gudanar da aikin,  inda jami’an su kuma suka mayar da martini da harba Barkonin tsohuwa don su fasa gungun na tsagerun.

 

Wani mai sanar Acaba ya bayyana cewa, an kuma ji harbe-harben bindigu a lokacin artabun.

 

Har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoton, Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar CSP Muyiwa Adejobi  bai fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.

Exit mobile version