Marafauta na jihohin Yamma sun gabatar da taro a yankin Abatuwa da ke Legas.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban mafarauta na Legas Olu Ogunronbi, ya nuna farin cikinsa ga wannan taro ya kuma roki jama’a a hada kai a zauna lafiya. “Mu marafauta kanmu a hade yake mun kiyaye duk abin da muka sa gaba Allah ya sa mu samu daurewa, shugaban mafarauta na yankin Legas ya kara da cewa kowa ya tabbatar mai farauta ya mallaki katin shaida, motocin zuwa farauta su tabbatar sun sa shaida a gaban motarsu domin kowa ya sani.
Saboda haka ya gode wa shugabannin Arewa da suka hada wannan taro.
Shi kuma a nasa jawabin, sarkin dawa na Arewa da ke Legas Alhaji Kabiru Ori ya yi farin ciki da ganin shugabanni daban-daban su ka zo wannan taro, kuma Sarki Kabiru ya kara cewa a shirye dokokin da aka shinfida kuma za su ci gaba da tattaunawa da jama’arsa, saboda haka ya gode, Allah ya mai da kowa gi da lafiya.
Shi kuma a nasa jawabin Alhaji Ado Shu’aibu Dansodo daya daga cikin manyan shugabanni a Legas ya yi farin ciki da wannan taro ya kuma nemi a zauna lafiya. Kabiru ya kara da cewa tsakanin mafarautan Arewa da abokanan zamansu na yamma akwai kyakkyawar fahimtar juna.
Shi kuma a nasa jawabin, mai masaukin baki Alhaji Danjuma Abatuwa Lagos ya yi godiya da wannan taro inda ya bayyana cewa ya ji dadi an zo lafiya an kuma tashi lafiya.
Daga cikin mutanan da suka zo akwai Olu Ogunronbi Abinbun, Aguniyi Babagun, Rasaki Shoetan, Akintunde Haruna, Ganiyu Aladajo. Sauran su ne: Abubakar Mogaji, Alhaji Ado Shuaibu, Kahlid Chitansi, Danlifi Baban Rabi Kaura Gezawa da kuma Alhaji Sani Wambai.