An Yi Bikin Ranar Mata Ta Duniya A Jihar Bauchi

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Kasancewar majalisar dinkin duniya ya ware kowace ranar takwas ga watan maris na kowace shekara a matsayin ranar mata ta duniya, maaikatar mata da hadin guiwar ofishin uwargidan gwamnan Jihar Bauchi da kungiyar Oxfam me taimakawa mata daga kasar Canada, sun shirya bikin ranar matan a gidan gwamnatin jiha a ranar alhamis da ta wuce inda aka gayyaci matan daga sassa dabam dabam na Jihar Bauchi kuma aka basu kyaututtuka a matsayin tallafi.

Uwargidan gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar, cikin jawabinta ta yaba da irin gudummowar da mata ke bayarwa wajen cigaban alumma tare kuma da bayyana irin ci gaban da mata suka samu a cikin wannan gwamnatin musamman bayar da horo kan koyon Sana’a da ba da tallafin naira dubu biyar ga mata matasa aikin yi da sauran su.

Madam Lydia Shehu darakta a maaikatar mata a jihar Bauchi cikin jawabinta ta bayyana cewa akwai matsaloli masu yawa da mata ke fiskanta a wannan lokacin, don haka ta ja hankalin mata da su himmatu wajen ganin sun kawo karshen matsalar musamman kan batun neman ilmi.

Saboda idan mace ta yi karatu ba sai an ce ta kai yaronta asibiti ba, kuma tasan yadda zata kayyade iyalinta ba tare da yin kunika ko ta tara yara ta bar su kara zube cikin wahala ba. Don haka ta bukaci matan jihar Bauchi su gode wa gwamnati na bayar da kudi naira milyan 190 don amfani da su wajen kare lafiyar mata daga rasuwa a lokacin da su ke da juna biyu.

Harwa yau ta koka da yadda ake tsangwamar mata idan an ba su matsayi yadda mata da kan su ke illatawa ko bata sunan yan uwansu. Don haka ta bukaci su yi hakuri da juna don samun ci gaba, don haka ta bukaci matan su rika isar da kukan su ga kwamishinar mata da sauran masu rike da mukamai matan da ke cikin gwamnati.

Lydia Shehu ta nemi mata da su daina mayar da kansu baya saboda suna da kokari wajen daukar ciki wata tara su kwana da shi su tashi da shi har su sauke. Don haka ta bukaci su zauna da juna lafiya su ci gaba da kokarin ganin sun ciyar da kan su da iyalen su gaba.

Kasancewar kungiyar Odfam ta shirya wannan taron ranar mata, Madam Hannatu John ta bayyana irin temakon da kungiyar odfam ta musu wajen ilmantar da su yadda ake nomar masara mai kyau inda suke samun amfani mai yawa ta hanyar bita kan noma da ba su irin shuka na zamani me yi da wuri.

Itama uwargidan mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Fatima Nuhu Gidado cikin jawabinta ta, ta godewa Allah game da sake ganin bikin ranar matan da ake gudanarwa a kowace shekara. Ta ja hankalin matan su tashi tsaye wajen neman abin kan su don ci gaba tare da kare martabar iyalan su. Inda ta bayyana cewa wannan ranace da aka ware domin mata su tattauna kan matsalar da ke damun su ko ina a cikin duniya.

Shugabar matan jamiyyar APC a jihar Bauchi Hajiya Saadatu Mahmud cikin jawabinta ta yaba game da nada kwamishinoni mata uku a jihar Bauchi kuma ta ja hankalin mata da su wayar da kan jamaa wajen fitowa su shiga a dama da su a harkar siyasa. Ta kira mata su fito a fafata da su a siyasa, saboda duk Arewa maso gabas mata biyu ne a majalisun jiha mace daya a tarayya. Don haka uwargidan shugaban kasa a zaman da suka yi a Abuja ta nuna damuwa saboda ganin mata dayace ke wakiltar matan jihohi 19 na Arewa a majalisar dattijai ta tarayya. Don haka ta bukaci su mika sakonta ga matan Arewa da dukkan matar da ta cancanta ta fito don tsayawa takarar kowace kujerar siyasa.

Mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado shine ya wakilci gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar, inda cikin jawabinsa ya yaba da ware wannan rana da majalisar dinkin duniya ta yi don tuna halin da mata ke ciki a duniya. Don haka ya yaba wa matan game da irin tallafin da suke ba mazaje don ci gaba a harkokin su ta hanyar kara musu karfin guiwa don samun nasara kan duk wata hidima da suka sa a gaba. Don haka ya bayyana cewa wannan gwamnati na ba mata muhimmanci musamman ta hanyar inganta ayyukan hukumar mata da matasa ya BACYWORD inda kuma basu fifiko a shirin daukan aiki na Npower da kuma daukan mata don ciyar daliban makarantun firamare shirin da ya taimaka wajen sama wa mata ayyukan yi don tallafawa iyalan su.

Exit mobile version