An Yi Bikin Yaye Dalibai A Karamar Hukumar Zango

Wata cibiyar koyar da sana’o’in hannu da ke karamar hukumar Zango ta yaye dalibai kimanin dari da goma sha shidda.

Daliban da aka zabo daga kananan hukumomi biyar biyar na masarautar Daura, sun samu horo akan sana’o’in hannu iri daban-daban domin zama masu dogaro da kansu.

Da yake magana, Murkan Daura Hakimin Zango Alh. Muhammad Hafiz Adamu, bayyana muhimmancin sana’o’in hannu ga dimbin matasan da ke yankin.

Alhaji Muhammad Adamu wanda kuma shine shugaban taron, yayi kira ga daliban da aka yaye da su yi amfani da abinda suka koya a ibiyar.

Kamar yadda yace, shirin horar da mutanen akan sana’o’in hannu, ko shakka babu taimaka masu wajen zama masu dogaro da kansu su kuma zama masu amfani a cikin al’umma.

Da yake magana, Magajin Garin Daura, Hakimin Fago ya yaba ma kwazon Dan Masanin Daura Alh. Sani Zango dangane da samar da cibiyar koyon sana’o’in a garin na Zango.

Ambassador Kabir Ahmed yace an nada kwamitin mambobi shidda da zasu lura da tafiyar da cibiyar.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da kuma masu hannu da shuni da su tallafama cibiyar domin habbaka ayyukanta.

Tunda farko, shugaban cibiyar Alh Mukhtar Yaro yace cibiyar bata samu sukunin yaye dalibanta su kimanin dari biyu ba, wadanda a da ta tsara zata yaye saboda karancin kudi da take fuskanta.

Ya bayyana cewa an bayar da dan tallafin fara sana’a ga dukkanin daliban da aka yaye domin su kafa wuraren sana’o’insu.

Da take magana daya daga cikin daliban da aka yaye Jamila Rufa’I ta godema mahukuntan cibiyar akan samar masu da da kayayyakin fara sana’o’I bayan kammala samun horon.

Exit mobile version