Daga Yusuf Abdullahi Yakasai,
Bikin yaye dalibai wani muhimmin al’amari ne ga kuma matukar darajar shi, ganin cewar su wadanda aka gabatar watarana sune manyan gobe, da za su Shugabanci, wurare daban- daban.
Wannan dalilin nema ya sa Shugaban taro Uban Sarkin Hausawan Agege mai martaba Alhaji Musa Dogon kadai, ya bayyana farin cikinsa da kan ganin wannan muhimmiyar rana mai tarihi.
Ya yi godiya ga shugabannin ita makarantar, ganin yadda dalibai suke karatukamar yadda ya dace, ya kuma roki Allah shi taimakesu, da kara jan hankalin dalibai su kara himma wajen karatun su.
Shi ma Shugaban makarantan Alhaji Yusuf Jibrin Isah Mai dankali ya yi godiya ga manyan baki da suka samu damar hallarar yaye daliban makarantar Babin Neef.
Ya ci gaba da jawabinsa inda yace wannan makaranta ta fuskantar matsaloli masu yawa can a baya. Yanzu Allah ya taimaka wajen kawo taimako ta shawo kan wasu daga cikin matsalolin.
Har ila yau Shugaban ya yi kira da iyayen yaro, su rika turo ‘ya’yansu makaranta da wuri, su kuma lura da ya’yan su wajen tambayarsu abubuwan da malaman suke koya ma ‘ya’yan su.
Daga karshe an rabawa dalibai kyaututuka, da kuma shedar takardar kammala karatun. Ya kuma roki su dalibai su kasance masu biyayya da ladabi, da kuma su zama masu koyi da abinda aka koya masu a makaranta.