Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Wasu masu Garkuwar da mutane dauke da muggan makamai a ranar Larabar data gabata suka yi garkuwa da wani dan kasuwa a Karamar Hukumar Minjibir mai tsawon kilomita 50 daga kwaryar birnin.
‘Yan bindigar sun dirarwa kauyen da misalin karfe 1:00 na talataunin dare, inda suka Yi ta harbin iska kusa da kauyen maska kafin daga bisani suyi awon gaba da dan Kasuwar mai suna Abdullahi Kalos.
Shaidun gani da Ido sun shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kuma kai farmaki ofishin ‘yan Sandan tare da kona motar ‘yan Sandan yankin.
Tun misalin karfe 4:20 na a subahi ‘yan bindigar suka yiwa ‘yan Sandan kwanton bauna kusan da makarantar firamare. A cikin motar ‘yan Sandan, akwai shikan sa DPO tare da sauran jami’ansa.
“Lokacin da ‘yan Sandan suka yi kokarin mayar da martani, nan take suka bankawa motar ‘yan Sandan cikin gaggawa.”
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan Sandan sunzo a cikin motar kirar Hilud, Bolkswagen, Sharon da Babura masu yawa.
Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa adadin ‘yan bindigar da yawansu ya tasamma mutum 30 sunfi karfi Jami’an ‘yan Sanda wanda hakan tasa dole suka tsallake suka bar motarsu. Majiyar ta ce ba’a samu daukin ‘yan Sandan karta kwana ba akan Lokaci.
Dan Kasuwar sananne a garin wanda ke sana’ar sayar da kayan gini da kayan Abinci, in ji majiyar.
“’Yan bindigar sun gudu sun bar daya daga cikin motocinsu sun tsere da kafa,” a cewar majiyar.
An yi ta kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa Amma ya nuna cewa Yana cikin mitin kamar yadda yadda ya yi alkawarin amsa kiran manema lambaran Nan bada jimawa ba.