Rabiu Ali Indabawa" />

An Yi Garkuwa Da Ma’aikatan Agaji 10 a Jamhuriyyar Nijar

An yi garkuwa da ma’aikatan agaji 10 a kudu maso yammacin kasar Nijar yayin da suke raba abinci a wani kauye.

Masu bayar da agajin na aiki ne a karkashin shirin agaji na ‘Action and Impact’ da ake kan yi a yankin Sahel.

Mai magana da yawun kungiyar Action and Impact Kadidiatou Harouna ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa ce maharan sun dira kauyen ne kan babura dauke da makamai inda suka yi awon gaba da ma’aikatan agajin.

Wannan ne karo na farko da aka sace masu ba da agaji a yankin Tillaber, wajen da aka umarce babura su daina aiki tun watan Janairun 2020.

Haka ma sun sace motoci kirar Jeep guda biyu.

Ana samun yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a yankin Sahel, musamman kan iyakar Mali da Burkina Faso.

A bara kadai an kashe sama da mutum 4,000 a yankin. A shekarar 2008 ma an sace wani ma’aikacin agajin Jamus da kuma wani malamin kirista na Italiya a yankin.

Exit mobile version