Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mai yi wa ƙasa hidima da ɗalibi mai matakin aji 300 na Jami’ar Jos.
An yi garkuwa da su ne yayin da wasu ‘yan bindiga suka afka wani gida a unguwar Dong da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
Mista Solomon Dansura, wanda aka yi garkuwa da sirikarsa da wani bako, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata a Jos.
Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun afka gidansa ne a daren Lahadi a lokacin da mazauna gidan ke shirin kwanciya barci.