An Yi Jana’izar Hadimin Shehu Ibrahim Niass, Musa Ghana, A Kaduna

Daga Abdulrazak Yahuza Jere

Dubun dubatar al’ummar Musulmi na cikin garin Kaduna da kewaye da makotan jihohi sun halarci jana’izar daya daga cikin hadiman sanannen shehin Musuluncin nan, Shehu Ibrahim Niass, Sheikh Musa Ghana, wanda ya riga-mu gidan gaskiya da maraicen Asabar din nan da ta gabata.
Sheikh Musa Ghana ya rasu ne sakamakon wata ‘yar kankanuwar jinya a yayin da ake kan hanyar kai shi asibiti.
daya daga cikin yayan Shehu Ibrahim, Sheikh Abdul’ahad Niass ya jagoranci jana’izar marigayin a Unguwar Malali da ke gabashin garin Kaduna, bayan sallar Azuhur ta jiya Lahadi.
Da yake gabatar da takaitaccen jawabi game da marigayin, Sheikh Abdul’ahad Niass ya bayyana cewa “Zakiru Musa Ghana tun yana dan shekara 20 ya zo wurin Shehu a Senigal, bayan ya yi shekara uku sai ya tafi, da Shehu ya sake dawo da shi sai da ya shekara 20 tare da Shehu, har sai zuwa lokacin da Shehu ya bar duniya… Duk inda Shehu zai je, in dai a Senigal ne to za ka ga Musa Ghana a gaban mota. Shi ne yake rike sandar Shehu. A lokacin da Shehu Ibrahim zai yi tafiyar Landan (jinyarsa ta barin duniya), ya yi wa Musa Ghana wasiyya, ya ce masa; Musa zan je amma zan dawo, sai dai ba irin dawowar da kuke so ba!”.
Shehu Abdul’ahad ya kuma yi waiwaye game da rayuwar da suka yi da marigayin tun daga Senigal har zuwa lokacin da suka sake haduwa gabadaya a Nijeriya kuma duka a Kaduna.
Shehu Musa Ghana dai an haife shi ne a ranar 7 ga watan Maris na Shekarar 1951 a kasar Ghana.
Ya rasu ya bar mata da yara, inda aka binne shi a makabartar musulmi da ke Unguwar Malali Kaduna.
Shehunnai da malamai da suka halarci jana’izar daban-daban sun bayyana alhinin rasuwarsa tare da nunar da cewa an yi babban rashi bisa la’akari da irin kokarinsa na hidimta wa Addinin Musulunci.

Exit mobile version