An Yi Jana’izar Janar Ahmed, Wanda Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Abuja

Janar Ahmed

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, an yi jana’izar Manjo Janar Hassan Ahmed, tsohon Probost Marshal na sojojin Nijeriya da aka kashe a ranar Alhamis a Abuja.

An binne Ahmed ne a ranar Juma’a dauke da cikakkun launuka na soja da yabo a makabartar ‘Guards Brigade, Lungi Barracks’ da ke Abuja, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Jana’izar ya gudana ne a lokacin da ‘yan uwa da abokan aiki ke zubar da hawaye.

Janar din sojin, mamba ne na kwas na 40, wanda ala kashe shi a wani kwanton bauna da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a kan hanyarsa daga Lokoja zuwa Abuja a daren Alhamis a kusa da Abaji, kusa da Abuja.

‘Yan uwansa wadanda ke cikin motar tare da ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shi yayin da direbansa ya tsere.

Da yake magana a lokacin jana’izar, Shugaban hafsan sojojin kasa, Laftana Janar. Faruk Yahaya, ya bayyana mutuwar Ahmed a matsayin babban rashi ga sojojin Nijeriya da ma kasa baki daya.

Yahaya ya bayyana Ahmed a matsayin hafsa nagari mai kwazo da jajircewa ga aikin sojoji da yi wa kasa aiki.

Ya kara da cewa, cikin ikon Allah ga jami’in ya mutu a lokacin da ya yi, ya ce, babu wanda ya san lokacin da kuma inda zai mutu.

Yahaya ya ce, duk wani mai rai shima ya san cewa zai mutu, sai dai kawai ya yi addu’ar neman gafara tare da tallafa wa dangin, yana mai alkawarin cewa rundunar za ta ci gaba da kasancewa tare da dangin marigayin

“Dole ne mu tsaya tare da kuma kula da danginsa a cikin wannan lokacin bakin ciki. Sojojin suna da tanade-tanade a dokokinmu dangane da hakki da sauran ayyuka kuma mun cika hakan. Bayan wannan kuma, rundunar, a karaashin kulawa ta, za ta inganta kan wadannan tanade-tanade kuma za su kasance tare da dangin marigayi Janar din. Ahmed aboki ne kuma abokin aiki kuma mun dade muna tare. Ya kasance mai kiyayewa, mai kula da aiki da kwarewa amma kowa yana da lokacinsa,” in ji shi.

Ya ce, “a madadin Babban Kwamandan Sojoji, hafsoshi da sojojin Nijeriya, muna mika ta’aziyya tare da iyalan marigayi Manjo Janar Ahmed.”

Yayin karanta jana’izar marigayi Janar din, Babban Manufa da tsare-tsaren Sojoji, Manjo Janar Anthony Omozoje, ya ce, Ahmed kwararren jami’i ne.

Omozoje ya ce, marigayi Ahmed ya yi aiki a wurare daban-daban kafin ya zama babban hafsan sojojin kasa.

Ya bayyana cewa, marigayi babban hafsan ya kasance Daraktan kula da harkokin tsofaffin Sojoji ne kafin rasuwarsa.

Exit mobile version