An Yi Kira Ga Amurka Da Ta Maida Hankali Ga Batutuwan Kare Hakkin Bil Adama Na Cikin Gidanta

Amurka

Daga CRI Hausa

 

Wasu rahotanni daga kafofin watsa labaran Amurka, sun nuna cewa, kaso 69 bisa dari na Amurkawa na da yakinin cewa, nuna wariyar launin fata na cikin manyan matsalolin dake addabar kasar, kana kaso 60 bisa dari sun amince da cewa, wannan matsala na kara kazanta sama da yadda abun yake shekara 1 da ta gabata.

Da yake tsokaci kan hakan, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa na yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce wariyar launin fata babbar cuta ce da ta dade tana addabar al’ummun Amurka, ta kuma kasance babbar matsala a fannin kare hakkin bil adama a kasar. Don haka fatan shi ne, Amurka za ta fuskanci abun da ke gaban ta game da kare hakkokin bil Adama.

A daya bangaren kuma, Wang Wenbin ya ce a tsawon lokaci, wasu Amurkawa na kara kaimin amfani da siyasa a matsayin makami na sauya gaskiya, game da asalin cutar COVID-19. Kuma irin wadannan mutane ba abun da suke fatan cimmawa, illa dorawa Sin alhakin gazawar hukumomin Amurkan, ta yakar annobar yadda ya kamata.  (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version