Connect with us

RAHOTANNI

An Yi Kira Ga Dan Majalisar Tarayya Alhaji Muntari Dandutse Ya Fito Takarar Kujerar Sanata A Yankin Funtuwa

Published

on

Anyi kira ga zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Funtuwa da Dandume a majalisar wakilai da ke Abuja Alhaji Muntari Dandutse da ya fito takarar Sanata a yankin Funtuwa.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin wata kungiya ta gamayyar matasa dake yankin Funtuwa kananan hukumomi 11 jim kadan da kammala taron su da suka yi a karamar hukumar Funtuwa a ranar Asabar, shugaban kungiyar hadakar matasan kananan hukumomi 11 Alhaji Aminu Albasu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai dalilin su na yin kiran Alhaji Muntari Dandutse da ya daure ya amsa kiransu ganin yadda yake da tarihin siyasa kuma yake taimakon al’umma da yawan ziyartar mazabar shi a lokaci daban daban, Alhaji Aminu ya ce, yasan irin gagarumin cigaban da Alhaji Muntari ya kawo ma karamar hukumar mulki ta Funtuwa a lokacin da ya yi shugabancin karamar hukumar sau biyu babu shakka ya dauki matasa aiki sama da matashi 200 ya kuma samar wa matasa jalin sana’oi domin su dogara da kawunansu, ga manyan aiyuka da yayi ma jama’ar karamar hukumar.
Alhaji Albasu ya ce, yasan Alhaji Muntari mutun ne haziki kuma mara tsoro mai kaunar masu sonshi da jajircewa wajen yi wa al’umma aiki, ya ce, kwanan nan suka gama rangadin gano manyan aiyukan da Alhaji Muntari ya yi wa karamar hukumar Funtuwa.
Saboda wannan cancactar tashi yasa muka yi wannan taro da sama da mutane 110 muke kira gareshi ya fito mana takarar kujerar Sanata ta yankin Katsina ta kudu Funtua Senatorial zone.
Shugaban kungiyar yace kowacce karamar hukuma muna da mambobi sama da mutum 200 kuma akwai shuwagabannin a kowacce mazabar kansila na kananan hukumomi 11 kuma akwai wakilcin dattawa da na mata, ya cigaba da cewar baza su daina kira ga Alhaji Muntari ba sai lokaci yayi da zai amsa kiran al’umma yace babu shakka an bar yankin Funtuwa a baya rabon da ayi wani abin arziki ko kawo wani gagarumin aiki tun lokacin tsoho watau sanata Abu Ibrahim. Allah yayi mashi Albarka ya bashi wata kujerar amin.
Alhaji Aminu ya ce, wannan kungiyar sune suka kafa abinsu kuma suna tara kwabo da tari domin tafiyar da wannan kungiya masu mambobi da yawa. Ya ce, shi kanshi Alhaji Muntari bai san da wannan kungiya ba saboda sune suka kafa kungiyar musamman masu son ci gaban yankin Funtuwa watau yankin Karaduwa. Ya ce, za su cibaga da wayar da kan jama’a muhimmancin Alhaji Muntari Dandutse a kan wannan kujera. Ya ce, suna mika godiyarsu ga Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari da Shuwabannin jam’iyar APC na yankin Funtuwa da jiha baki daya.
Advertisement

labarai