Shugaban kungiyar Direbobi ta kasa NURTW reshen Jihar Kaduna, Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i da ya gargadi hukumar kula da gine-gine ta Jihar da ke rushe tashar mota, ba tare da yi wa dimbin jama’a tanadin wurin da za su zauna domin ci gaba da sana’o’insu ba.
Alhaji Aliyu Tanimu Zariya, ya yi wannan kiran ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kaduna.
Shugaban NURTW reshen jihar Kaduna ya shaida wa manema labarai cewa su a kodayaushe masu yin biyayya ne ga Gwamnati, don haka suke bayar da shawarar cewa idan za a rushe Tashar mota, to a yi kokarin sama wa dimbin ‘ya’yan kungiyar da ke neman abin da za su ci tare da iyalansu wurin da za su koma domin ci gaba da sana’arsu.
“An rushe tashar Unguwar Talbishin da ake kira talbishin/ Kakuri, bayan an rushe sai aka ce masu su koma KSTA, amma kuma wanann wuri ba gyara, ba wutar lantarki, ba ruwa, ba tsaro, saboda haka ta yaya jama’a za su kai dukiyarsu a wannan wuri. Ko su ‘ya’yan kungiyarsu su koma domin ci gaba da gudanar da sana’arsu a wurin,” ya tambaya.
Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya kuma bayyana goyon bayansa ga Gwamnatin Jihar, wanda dalilin hakan ne ma ya sa suke kokarin sayar da rasidin gwamnati a dukkan tashoshin motocin da yake suna gudanar da sana’arsu ta tuki tsawon shekaru da dama.
Ya ce, “muna kuma maraba da shirin Gwamnati na kokarin duba lafiyar direbobi idan lokacin hakan ya zo, amma muna jiran umurnin uwar kungiya ta kasa a kan wannan batu.”