Connect with us

RAHOTANNI

An Yi Kira Ga Gwamnati Da Ta Taimaka Wa Iyalan Jami’an Tsaron Da Suka Rasa Rayukansu

Published

on

An yi kiran gwamnatin tarayya da ta taimakama iyalan jami’an tsaron da sukarasa rayukansu wajen yima kasa aiki,

Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin NAK kuma shugaban kwamitin bunkasa dangartaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma PCRC na shiyyar Funtuwa.

Alhaji Akilu Babaye jim kadan da kammala taron masu ruwa da tsaki na kwamitin a ranar Larabar da ta gabata a ofishin baturen ‘yan sanda na shiyyar Funtuwa Area Commander dake Funtuwa a jihar Katsina.

Alhaji Akilu ya yaba ma kwamitin bunkasa dangantaka tsakanin ‘yan sanda da jama’ar gari ganin yanda mutane ake samun karin dangantaka tsakaninsu da fahimtar juna don ta hakane kawai dan sanda ya zama abokin kowa banda mai aikata laifi kuma akoda yaushe ake kara zakulo marasa gaskiya.

Alhaji Babaye ya ce, yana kara kira ga al’umma dasu kara ba jami’an tsaro goyon baya don gudanar da aikinsu kamar yanda ya kamata saboda masu iya magana suna cewa da dan gari akan ci gari wajen zakulo mutane marasa gaskiya, shi dan sanda yazo aiki ne domin kare rayukan jama’a tare da dukiyoyin su don haka ba abokin gaba bane, ta haka ne za’a magance rashin tsaron dake damun wannan yanki namu kuma jama’a suci gaba da taimakon yan sanda ta hanyoyi da dama wajen kai labarin bata gari da bayar da shawarwari masu ma’ana ganin yadda aka yi sa’a domin an sami Area Commander nagari mai son yankin Funtuwa da jiha da kasa baki daya kuma bugu da kari aka samu sauran jami’an yan sanda na kirki irinsu D.P.O. Na CPS Funtuwa da Makera, Bakori, Danja, Faskari, Dandume, Sabuwa da sauran yan sanda na yankin Funtuwa.

Alhaji Akilu ya gode ma sauran mambobin kwamitin PCRC na kananan hukumomin Funtuwa, Faskari, Danja, Bakori, Dandume da na karamar hukumar Sabuwa wajen kokarinsu da ba ‘yan sanda yankin goyon baya, yace babu shakka Area Commander yayi kokari sosai wajen ba wannan kwamitin goyon baya da kara wayar da kan kwamitin su a ko da yaushe.

Daraktan kamfanin NAK Alhaji Akilu yayi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta duba kuma ta kara dubawa wajen biyan hakkokin iyalan jamian tsaron da suka rasa rayukansu wajen yi ma kasa aiki watau wadanda suka rasu wajen aikin kare rayukan jama’ar kasar nan da dukiyoyin su ya kamata ace kafin wadan da suka mutu wajen bautar kasa su cika kwana 7 da rasuwa gwamnati ko hukumar yan sanda ta kasa su biya wadan nan bayin Allah hakkokinsu don tallafa ma iyalansu kada su tagayyara, babu shakka akwai tausayi sosai ganin yadda iyalan jami’an tsaron da suka rasu wajen aiki suke komawa kafin a biyasu hakkokinsu wasu sai su kwashe shekara da shekaru ba a biyan su ba wasu yaran daga nan karatu ya gagaresu kenan sun shiga cikin wahala kuma yana kara rage kwarin gwiwar sauran jami’an tsaro wajen kare rayukan yan Najeriya da dukiyoyinsu kuma yana kara cin hanci da rashawa a tsakanin su jami’an tsaro yace da wannan kudin da a ka biya iyalan wasu zasu sayi gidan da zasu koma da sauran yaran kuma su biya kudin karatun yaran ya kamata gwamnati ta kare taimakon jami’an tsaro da suka rass rayukansu wajen aiki.

 

Daga karshe Alhaji Akilu yana kara mika godiyarshi ga gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Aminu Bello Masari ganin yadda gwamnatin shi ta gina kasuwa hade da tashar mota ta zamani a garin Funtuwa wannan abun a yaba ne kwarai don ya habbaka harkar kasuwanci a yanki saboda Funtuwa garin kasuwanci ne da noma sannan ya yabi shugaban kasa wajen aniyarshi ta taimakon al’ummar kasar kuma yana kira ga gwamnatin tarayya da ta kara tashi tsaye wajen magance harkar tsaro a yankin arewa musamman a jihar Katsina da yankin Katsina ta kudu kuma ya jajanta ma mutanen karamar hukumar Faskari da Sabuwa da sauran kananan hukumomin da rashin tsaro ya dama wadanda su ka rasu Allah ya jikansu, Allah yayi ma shuwagabannimu jagora.

Advertisement

labarai