An Yi Kira Ga Gwamnati Ta Rika Bai Wa Ma’aikatan Jinya Da Ungwar Zoma Kulawa

Zoma

Daga Ibrahim Muhammad,

An yi kira gwamnati ta rika sanya kungiyoyin ma’akatan lafiya a tsare-tsaren manufofinta na kula da fannin lafiya domin hakan zai taimaka sosai wajen cimma kyakkyawar nasara.

Shugaban Kungiyar ma’aikatan jinya da Unguwar zoma ta kasa reshen jahar Kano, Kwamared Ibrahim Maikarfi Muhammad, sh ne ya yi wannan kiran a yayin da yake jawabi a taron ranar makon ma’aikatan jinya da unguwar zoma na Duniya wanda ya gudana a harabar sakatariyar kungiyar na Kano.

Ya ce rashin sanya su a manufofi da tsare-tsaren gwamnati ya sa ana samun nahawu a wurin cimma abubuwan da ake bukata, wanda idan aka sami hakan zai zama babban abin da zai haifar da bunkasa harkar lafiya.

Kwamred Ibrahim Maikarfi, ya bayyana cewa matsalolin da ke damun fannin lafiya sun hada da na rashin isassun ma’aikata da kuma rashin kimanta su daga bangaren hukuma ta rashin bai wa ma’aikatan jinya da Unguwar zoma damar cancanta da suke da ita ta kwarewa wajen daukar su ayyuka a manyan cibiyoyin lafiya.

Don haka abin da yakamata a kawo gyara akan lamarin don taimaka wa bunkasa lafiya.

A yayin taron an yi tattaki na nuna amfanin ma’aikatar lafiya da motsa jiki.

Exit mobile version