Alhussaini Sulaiman" />

An Yi Kira Ga Gwamnonin Arewacin kasar Nan Da Su Samar Da Aikin Yi Ga Matasa

Wani basarake sannan dan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwar kantin kwari dake Kano, Alhaji Muhammadu Gambo danpas dansaran Kano, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnonin arewacin kasar nan da su masar da aikin yi ga matasan yankin.
Alhaji Muhammadu Gambo danpas, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Basaraken ya kara da cewa bayan sun samar wa da matasan aikin yi su kuma smar masu da wuraren koyon sana’oin dogaro da kai , tare da samr masu da ilimi ingantacce.
Natukar suka yi wannan babu shakka zai rage matsalolin da yankin na arewa ke fuskan ta musammam na rashi tsaro da sauran su da yardara Allah. Alhaji Gambo danpas ya kuma ya ba da yadda gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje akan yadda ya kara rana daya domin gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwan nin jihar yana fatan gwamnan zai ba da umurnin abude kasuwan nin gaba daya, idan ya yi haka tattalin arzikin jihar da kasa baki daya zai kara bunkasa da cigaba.
Da yake tsokaci game da cutar korona basaraken ya yi addu’ar allah ya gaggauta kawo mana karshen ta a jihar da kasar nan dama duniya bakidaya sannan kuma al’umma su kara kaimi wajen yawaita addu’a da kuma neman gafara ga Allah

Exit mobile version