Ibrahim Muhammad" />

An Yi Kira Ga Iyaye Su Kula Da Ilimi Da Tarbiyar ‘Ya’yansu

Alhaji Yusuf Ibrahim Wakilin Dukiya dan kasuwa kuma tsohon shugaban kungiyar masu musayar kudaden kasashen waje ta WAPA ya ja hankalin iyaye su rika jan ya’yansu a jiki ta basu kulawa akan neman ilimi da kyautata tarbiya, ya bayyana haka ne a wajen taron karramawa da Salka media ta yi a kwanakin baya.

Ya ce, bai kamata iyaye su rika sakin ya’yansu sakaka ba alhakin tarbiyya da ba su ilimi yana kansu kuma hakan zai kawo ya’ya su gane ana basu kulawa da suma idan suka taso zasu kula da iyayensu. Barin ‘ya’ya da ake sakaka shi yasa idan suka tashi basa ganin kimar iyaye saboda yaro ya tashi ba kulawa zai yi abinda yaga damane sai dai idan Allah ya hada shi da abokai nagari.
Ya ce, duk mai ‘ya’ya a wannan zamani yana cikin kalubale a cigaba da basu kulawa da yi musu addu’oi ba kawai naka ba duk ‘ya’ya na kusa dana makota a rungumesu a basu kulawa da tarbiya hakan zai sa ka gyara naka ka kuma gyara na wasu su zama masu amfanar al’umma.
Alhaji Yusuf Ibrahim wanda ya na daga cikin zababbun mutane da salka ta yi wa muhimmiyar karramawa ya bayyana jin dadinsa bisa karramawar, ya ce, nasarar hakan bata wuce yanda ake zaune da kowa lafiya ba a tsakanin al’umma bisa gaskiya da amana.
Ya kara da cewa wannan karramawa hukunci ne na Allah don haka yana mai gode wa Allah bisa karramawar, ya ce, wannan za ta kara masa kwarin gwiwa na cigaba da kyautata mu’amala domin kullum rayuwa tafiya take duk abin alkhairi da zaka yi wa dan Adam kayi masa don Allah.

Exit mobile version