Yusuf Abdullahi Yakasai" />

An Yi Kira Ga ‘Yan Arewa Mazauna Kurmi Su Hada Kansu

Wakilin Sarkin Hausawan Ijebo, Legas, Abdulhamid Ibrahim Gidderi,  ya nuna matukar farin cikinsa a bisa dawowar Shugaba Buhari bisa kujerar mulkin kasar nan a karo na biyu, yana mai rokon ‘yan Nijeriya da su taimaka masa da addu’a domin samun nasarar ayyukan da ya sanya a gaba. Sannan wakilin Sarkin Hausawan ya yi  kira ga matasa da su yi kokarin nemawa kansu ayyukan yi ta hanyar koyon sana’o’in hannu, ya kara da yin roko ga gwamnati da ta kara tallafawa matasan domin su ne manyan gobe.

Abdulhamid Ibrahim Gidderi, ya tabo wasu daga cikin ayyukan da yake son wannan gwamnatin ta karasa masu, kamar maganan yashe kogin Kwara da aka fara da sauran hanyoyin mota. Ya kuma nanata addu’an cewa, muna yi masa fatan alkhairi da samun nasarar wannan aikace–aikace da ake yi na alkhairi, ya kuma roki ‘yan arewa mazauna Kurmi a inda yake cewa, “ Ya kamata mu hada kanmu, mu zauna lafiya da abokanan zamanmu da muke tare a nan yammacin kasar nan, kuma mu kauce wa neman fitina da tashin hankali, saboda muna da shugabanni da za mu mika koken mu a wurinsu, ya kirayi shugabannin da su kara kwazo domin ganin komai yana gudana cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna.

A karshe, Abdulhamid Ibrahim Gidderi, ya yi fatan alkhairi ga Nijeriya da Jihar Lagas, tare da fatan Allah Ya ba mu zaman lafiya a kasa baki-daya.

Exit mobile version