An Yi Musayar ‘Yan Wasa Tsakanin Tottenham Da Sevilla

Tottenham

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki dan kwallon Sevilla, Bryan Gil sannan itama kungiyar ta bayar da dan wasa Erik Lamela cikin kunshin yarjejeniyar kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Gil, mai shekara 24 a duniya, ya saka hannu kan yarjejeniyar kakar wasa hudu, wanda ya fara yi wa tawagar Sifaniya wasa cikin watan Maris, yana cikin wadanda ke wakiltar kasar a Olympic a Tokyo a bana.

Sannan ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Sebilla wasanni 14 a gasar La Liga a matakin mai shiga wasa daga baya a matakin sauyi kuma rashin samun damar buga wasannin ne yasa ya yanke shawarar barin kungiyar.

Dan wasan tawagar Argentina, Lamela, mai shekara 29 ya koma kungiyar kwallon kafa ta Tottenham daga kungiyar Roma kan fam milyan 25.7 a shekarar 2013 kuma ya bugawa kungiyar wasanni da dama.

Lamela yana daga cikin ‘yan wasa bakwai da Tottenham ta dauka, bayan da ta sayar da dan wasa Gareth Bale ga Real Madrid kan fam miliyan 88 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Cikin ‘yan wasa bakwai da kungiyar mai buga Premier ta dauka sun hada da Christian Eriksen da Roberto Soldado da Paulinho da Etienne Capoue da Blad Chiriches da Nacer Chadli da kuma Erik Lamela.

Kawo yanzu Lamela shine na karshe da ya bar kungiyar daga jerin bakwan da ta saya, bayan sayar da Bale kuma ya ci kwallo 37 a wasanni 255, ya kuma yi zaman benci a wasan karshe a Champions League a shekarar 2019 da Liberpool ta lashe kofin.

Gil ya fara buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Sebilla daga matashi ya kuma fara buga wa babbar kungiyar wasa a watan Janairun shekara ta 2019 inda daga nan ne akayi masa rijista ta zama babban dan wasa.

Wasan karshe da ya yi mata ita ce a cikin watan Satumbar 2020 daga nan ya je Eibar, wadda ya yi wa wasannin a birnin rio na kasar Brazil  kuma ya ci kwallo hudu a wasa 28 da ya yi wa Eibar, wadda ta kare a matakin karshe a kasan teburin La Liga da aka kammala.

Tottenham tana ci gaba da bibiyar dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Atlanta, Romero, dan kasar Argentina domin ganin ya koma kungiyar kafin a fara kakar wasa mai zuwa a watan Agusta.

Amma yanzu kungiyar bata iya shawo kan kaftin dinta ba, Harry Kane, wanda ya bayyana cewa yana son tafiya inda zai lashe kofi kafin yayi ritaya daga buga kwallo kuma tuni kungiyoyi daban-daban a ciki da wajen Ingila sun nuna sha’war daukar dan wasan mai shekara 27 a duniya.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dain itace a kan gaba wajen zawarcin dan wasan inda ta kai tayin kudi fam miliyan 100 domin a sallama mata shi amma Tottenham din ta dage cewa ba zata sayar da Kane ba sannan kuma idan har ya zama dole sai ta sayar dashi dole duk kungiyar da take son sayansa ta biya fam miliyan 150 ko kuma ta hakura.

 

Exit mobile version