Daga Alhussain Suleiman Dakace,
Ganin yadda makarantu masu zaman kansu dake kasar nan ke taimakawa gwamnati da al’umma wajen samar da ilimi mai kyau da inganci tare da samar da aikin yi , yana da kyau gwamnatin tarayya da na jihohi su taimaka masu ta yadda za su ji dadin gudanar da aikin na samar da ilimi.Wannan kiran ya fito ne daga bakin shugaban kwaleji mai zaman kanta dake Kano, Aminu Kano College of Education ,Dakta Ayuba Ahmad Muhammad, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar kwalejin dake daura da shiga tsohuwar Jami’ar Bayero dake birnin Kano.
Dakta Ayuba Ahmad Muhammad ya ce wasu daga cikin tallafain da makarantun suke bukata tun daga Firamare, Sakandare Kwaleji, da Jami’a sun hada da ba su rance kudi mara ruwa, da kuma fili ga duk mai bukatar gina makaranta, tare da cire masu haraji. Dakta Ayuba Ahmad Muhammad, ya cigaba da cewa babu shakka shigowar ‘yan kasuwa wajen samar da makarantu masu zaman kansu abin farin ciki ne da alfahari, sannan kuma cigaba ne sosai wanda shekarun baya ba’a samu irin haka ba.
Idan aka lura makarantu irin kwalejoji da jami’a suna taka rawa sosai wajen samar da ilimi mai kyau, illa kawai rashin samun tallafi daga gwamnatoci, yana da kyau gwamnatocin su buda domin kowa ya anfana inji Malam Ayuba Ahmad Muhammad.Shugaban kwalejin mai zaman kanta yace daga lokacin da kasar nan ta fara mulkin Dimukaradiyya zuwa yau ilimi ya samu cigaba musamman an samu karuwar kwalejoji da jami’oi masu zaman kansu hatta ita ma gwamnati na cigaba da samar da karin jami’oi a daukacin kasar. Daga karshe ya godewa daukacin manya da kana nan malaman tare da ma’aikatan da suke aiki da kwalejin wajen musamman yadda suke bai wa hukumomin kwalejin hadin kai da goyon baya, su kuma daliban da suke karatu sai yi yi kira agare su da su cigaba da ba da himma da kwazo akan karatun su tare da ladabi da biyayya kamar yadda suka saba.