Abubakar Muhammad Taheer" />

An Yi Rangwamen Kudin Aikin Hajji A Jigawa

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta yi rangwamen kudin kujerar aikin hajjin bana daga Naira miliyan daya da dubu dari biyar da goma sha uku zuwa Naira miliyan daya da dubu dari hudu da sittin da hudu.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Hashimu Kanya, ya bayar da tabbacin cewa, ragin ya biyo bayan kokarin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar ne wajen tallafa wa maniyata.

Ya ce, za a mayarwa da maniyyatan da su ka biya kudin kujera Naira miliyan daya da dubu dari biyar da sha uku ragowar kudinsu Naira dubu arbain da tara da dari hudu da saba’in da biyar kafin tashi zuwa Kasa mai tsarki.

Alhaji Ibrahim Hashimu Kanya ya yaba wa Gwamna Badaru Abubabakar bisa kokarinsa na tallafa wa maniyatan jihar tasa.

Ya ce, hukumar ta kammala duk wani shiri na samun nasarar aikin hajjin bana.

Exit mobile version