Connect with us

LABARAI

An Yi Taro Masu Sauraron Rediyo Da Talabijin Na Liberty

Published

on

An gudanar da gagarumin taron sanin makamar aiki na yin rijistar kungiyar masu sauraron rediyo da talabijin na Liberty.
Shi dai wannan taron an yi shine a makarantar Firamare ta Utako cikin babban birnin tarayya Abuja a karkashin Shugabancin Sa’idu Umar wanda kuma shine Shugaban ita kungiyar, wadda take da mambobin ta wadanda suke daga sassa daban- daban na birnin tarayyar, wadanda suma sun kasance a wurin  shi wannan taron.
Sakataren hadaddiyar kungiyar kwadago ko kuma United Labour Congress Comrade Nasiru Kabir shi ne babban bako wanda kuma ya ba kungiyar shawarwari, akan hanyoyin da za ta bi ta kai ga samun rajisata. A jawabin nasa ya bayyana hanyoyin da ita kungiyar zata bi domin ta samarwa mambobinta ayyukan tsira da mutuncinsu, wanda ma idan har a ka yi sa’a na iya samun aiki a karkashin gwamnati ko kuma wata Hukuma.
Bugu da kari kuma kamar dai yadda ya ce kungiya babu wani abinda yafi ta karfi a duniya, ya kara yin bayani inda yace cikin irin gudunmawar da ita kungiyar take badawa ta hanyar shawarwarin da suke ba kafofin watsa labarai yadda zasu inganta shirye- shiryen na su. Hakanan ma ya ce “Abubuwa da yawa suna faruwa a kasa, yawanci kuma sai ta kungiya ce ita gwamnati take sauraren mutane”. Sai ta hanyar kungiya ake samun hanyar cimma wasu manufofi.
Daga karshe ya yi kira da su mambobin kungiyar da cewar su yi ma Shugabannin su biyayya, kazalika suma Shugabannin su yi wa magoya bayansu adalci kamar yadda yakamata. Ya kuma har ila yau jan hankalin su ‘yan kungiyar, na cewar su lura sosai saboda wasu ‘yan siyasa na iya amfani da su, daga karshe a sake su a  igiyar ruwa.`
Kada kuma shi dan kungiya ya shiga kungiyar ne saboda kawai a taimaka ma shi, amma abinda a ka fi so shine shima ya taimaka ma wani ko kuma wasu. Sai kuma sun hada kai a matsayin su na ‘ya’yan kungiyar su samu a yi masu rajista wadda kuma sai sun hada da hakuri.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: