An Yi Taron Mu’amalar Jakadun Afirka Dake Sin Mai Taken “Kyakkyawar Jihar Xinjiang”

Daga CRI Hausa

A ranar 29 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin da gwamnatin jihar Xinjiang, sun kaddamar da taron mu’amalar jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin mai taken “Kyakkayawar Jihar Xinjiang,” a birnin Urumqi.

Jami’an diflomasiyya sama da 40 daga kasashe da yankuna 30 na Afirka sun halarci wannan taro.

A yayin taron, shugaban gwamnatin jihar Xinjiang Shohrat Zakir ya yi bayani kan wasu harkokin da suka shafi jihar.

A nasa bangare, shugaban tawagar wakilan, kana, jakadan kasar Kamaru dake kasar Sin, Martin Mpana ya ce, cikin ‘yan kwanakin nan, sun ziyarci wurare da dama a jihar Xinjiang, sun kuma kara fahimtar wannan wuri, kuma irin ci gaban da aka samu a jihar ya burge shi matuka. Al’ummomin kabilu daban daban suna zaman rayuwa cikin lumana, tattalin arzikin jihar na bunkasuwa da sauri.

Ya ce, sun ga kyakkyawar makomar al’ummomin jihar, suna kuma goyon bayan kasar Sin kamar yadda suka yi a baya.

A yayin taron, wasu ‘yan jihar Xinjiang da wakilan kungiyoyin addinai sun ba da misalai, yayin da suke bayani game da yadda aka raya harkokin samar da ayyukan yi, da ba da ilmi, da kare ‘yancin bin addinai a jihar, sun kuma zargi wasu kasashen yammacin duniya, dangane da jita-jitar da suke yadawa game da jihar, cewar, wai ana tilastawa al’ummomin jihar Xinjiang yin ayyuka, da rushe masallatai da sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version