Daga CRI Hausa
An yi taron yaba wadanda suke ba da babbar gudunmawa wajen kawar da talauci a kasar Sin a yau Alhamis a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taro tare da ba da jawabi.
Tun lokacin da aka kira babban taron wakilan jama’a karo na 18 na jam’iyyar JKS, Sin ta aiwtar da shirin yaki da talauci mafi girma da karfi a kasar. Shekaru 8 da suka gabata, an debi gundumomi 832 da kauyuka dubu 128 da ma manoma fiye da miliyan 100 da suka fama da talauci daga kangin talauci, matakin da ya zama abun ban mamaki ne a duniya wajen tallafin matalauta. Haka Sin ta cimma nasarar dakile matsalar kangin talauci, inda ta kafin shekaru 10 da cimma muradun kawar da talauci da MDD ta yi na shekarar 2030.
Xi Jinping ya ce, bayan gwagwarmayar da al’umomin kasar Sin suka yi, a gabanin cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar JKS, kasar ta cimma nasarar kawar da kangin talauci a dukkanin fannoni.
Xi Jinping ya bayyana cewa, talauci ba tsarin gurguzu ba ne, idan masu fama da talauci sun dade suna cikin kangin talauci, kuma babu kyautatuwar zaman rayuwa gare su, ba za a ce, tsarin gurguzu yana da wani fifiko ba, saboda haka, lamarin ba zai kasance wani yanayi na tsarin gurguzu ba.
Tun daga shekarar 2012 da aka gudanar da cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 18, kasar Sin ta fara mai da aikin kawar da talauci a matsayin babban burinta, domin fitar da dukkanin masu fama da talauci daga kangin talauci, inda a cikin ko wace shekara, ana ba da taimako ga mutane sama da miliyan 10 ta yadda za a fid da su daga kangin talauci, adadin da ya kai yawan al’ummar wata matsakaiciyar kasa.
Kuma cikin wadannan shekaru da suka gabata, yanayin tattalin arziki da zaman takewar al’ummar kasar Sin ya samu kyautatuwa matuka, musamman ma cikin yankunan da aikin kawar da talauci ya shafa.
Xi Jinping ya bayyana cewa kasarsa ta samar da wani tsari na “Sin abar koyi” a yaki da talauci, kana ta bayar da babbar gudunmawa a shirin yaki da talauci na kasa da kasa. Kuma ya jaddada aniyar shugabancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin CPC wajen yaki da talauci. ya yi kira ga sassan hukumomin kasar, da su zage damtse wajen aiwatar da matakan hade manufofin rage talauci da aka cimma a kasar da na raya karkara.
Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya bukaci da a ci gaba da mayar da batun magance matsalolin dake addabar fannin noma, da yankunan karkara, da manoma, a matsayin wadanda za a baiwa fifiko, cikin ayyukan da JKS ke gudanarwa. (Amina Xu,Maryam ,Ahmad, Saminu)