CRI Hausa" />

An Yi Taron Yayata Manufofi Na “Labaran JKS” Kan Xinjiang A Urumqi

Yau Litinin da yamma ma’aikatar cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da kwamitin JKS na yankin Xinjiang, sun shirya taron yayata manufofi mai taken “Labaran JKS” kan yankin Xinjiang cikin hadin gwiwa a birnin Urumqi, fadar mulkin yankin, inda baki sama da 300 da suka zo daga jam’iyyun siyasar kasashen waje da hukumomin kasa da kasa da kungiyoyi masu zaman kansu da kafofin watsa labarai da kungiyoyin masana kusan 200 suka halarci taron ta kafar bidiyo.

Babban taken taron shi ne “Samar da rayuwa mai dadi ga al’umma”, inda za a tattauna wasu batutuwa game da kare lafiyar al’umma. da yaki da talauci. da hada kan al’umma, musamman ma kan yadda kwamitin JKS na yankin Xinjiang yake tabbatar da manufofin raya yankin na JKS a sabon zamanin da ake ciki.
Wakilin sashen harshen Larabci na CGTN ya zanta da wasu shugabannin jam’iyyun siyasa da na kungiyoyi masu zaman kansu a Urumqi a daren jiya, inda baki mahalarta taron suka karyata matakan nuna fin karfi da wasu gwamnatoci da kafofin watsa labaran kasashen yamma suka dauka ta hanyar bayyana hakikanin abubuwan da suka gani da idonsu, kuma suka jinjinawa sakamakon da yankin Xinjiang ya samu wajen yaki da ta’addanci, kana suka yaba wa yankin saboda ci gaban tattalin arzikin da ya samu karkashin jagorancin JKS.
Yayin zantawarsu, babban sakataren jam’iyyar KKP ta kasar Iraki Kava Mahmoud ya bayyana cewa, ta’addanci makiyayi ne na duk duniya, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan da suka dace a yankin Xinjiang, kuma ta samu babban sakamako a fannin, ya ce, ya taba ziyartar Urumqi a ‘yan shekarun da suka gabata, kuma ya san kundin tsarin dokokin kasar Sin ya tabbatar da ‘yancin bin addani a kasar, kuma ba a siyasantar da addini a kasar Sin ba.
Babban sakataren kungiyar sada zumunta tsakanin kasar Sin da Sri Lanka Rathindra Kuruwita shi ma ya bayyana cewa, kafofin watsa labaran kasashen yamma, kafofin nuna fin karfi ne, a don haka ya dace a kara tantance ainihin yunkurinsu.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version