Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

An Yi Wa Mutum 3,509 Gwajin Korona A Nasarawa – Kwamishina Baba Yaya

by
2 years ago
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Karakainar Gwajin Cutar Korona A Nijeriya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Nasarawa, Famasi Ahmad Baba Yaya, ne ya bayyana wa manema labarai haka a ofisinsa da ke garin Lafia.

Kwamishinan ya ce a dukkan  gwaje-gwajen da gwamnatin jihar ta yi domin dakile yaduwar annobar cutar Korona a Jihar, akalla an yi wa kimanin mutane 3509 a Jihar gwajin.

Ya ce an kuma samu masu dauke da cutar Korona da yawansu ya kai kimanin 400 da wani abu. Kuma an kwantar da su a Asibitocin da aka kebe domin jinyar masu dauke da cutar.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

Bayan ba su kulawa da magunguna mutum 350 sun samu lafiya har an sallame su sun koma gidajen su. Sannan kimanin mutane 13 suka rigayemu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da wannan cutar, cikin su har da dan Majalisar dokokin jihar Nasarawa.

Yanzun akwai mutum 16 da suke kwance a Asibiti suna karban magani. Duk wanda ya ji sauki muna sallamar sa ya tafi gida ya ci gaba da aikin sa. akwai wadanda su na gidajensu, amma muna kara bibiyansu muna duba jikinsu.

Idan ka duba za ka ga cewa Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi matukar kokari wajen dakile yaduwar annobar cutar a cikin Jihar. Kuma jihar ta yi namijin kokari wajen kulawa da al’ummar jihar domin samar da kariya domin dakile yaduwar cutar.

Kwaminshinan ya kara da cewa, duk ma’aikacin jinya da ke karkashin gwamnatin bai kamata a ce lokacin aiki ya bar Asibiti ya je wani guri na kashin kansa ba.

Za mu sanya ido duk wanda muka kama shi ya bar Asibiti a lokacin aikinsa ya je wani Asibiti ko nashi ko na ‘yan kasuwa yana aiki a cikin lokacin aikin gwamnati za mu hukunta shi.

Mun san cewa aikin Asibiti yana da bangarori da yawa, amma dole ne malamin jinya ya tsaya a bakin aikinsa har sai lokacin tashin sa ya yi sai ya je wani gurin da yake aiki.

Wannan dokan aiki ne a ko ina, ba sabon tsari ba ne, kuma za mu tsaya tsayin daka mu tabbatar da an yi amfani da wannan dokar a dukkan Asibitocin gwamnatin jihar Nasarawa.

Komai ya na da dokoki, sai dai akwai kwararrun Likitocin da dole ka kyale su saboda ana bukatar su a ko’ina, kuma ire-irensu ba su da yawa a yanzu, kuma aikin da suke yi ba kowa ne ke iya yi ba.

Idan mutum ya tashi daga aiki domin kowane aiki akwai tsarin awowin da ma’aikaci zai dauka a bakin aiki. Idan mutum ya tashi a madadin ya je gida kawai ya kwanta yana iya zuwa wani gurin ya yi aiki saboda kasan nan ana fama da karancin Malaman kiwon lafiya ko ta ina.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Talaka Ne Zai Sha Azabar Karin Farashin Litar Mai – Dakta Makarfi

Next Post

Hon. Gazali Ya Zama Shugaban PDP Na Kware

Labarai Masu Nasaba

Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Kama  Wasu Sojoji Masu Hulda Da ‘Yan Ta’adda

by
1 year ago
0

...

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

by
1 year ago
0

...

APC

Sanata Al-Makura Ya Cancanci Rike Kujerar Shugabancin APC, Inji Gwamna Sule

by
1 year ago
0

...

Kebbi

Bagudu Ya Bukaci ’Yan Nijeriya Su Zama Masu Kishin Kasa A Shafukan Sada Zumunta

by
1 year ago
0

...

Next Post
Ta'addanci

Hon. Gazali Ya Zama Shugaban PDP Na Kware

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: