Bello Hamza" />

An Yi Wa Sabbin Cibiyoyin PoS 75,637 Ragista A Shekarar 2018

Bincike ya nuna cewa, an yi wa cibiyoyin PoS 75,637 a fadin tarayyar kasar nan don ci gaba da gudanar da hular kudade a shekarar 2018.
Hakan ya nuna an samu cibiyoyin da suka kai 258,443 ya zuwa watan Disamba na shekarar 2018, kamar yadda bayanai daga hukumar ‘Nigeria Inter-Bank Settlement Scheme’ ya nuna.
Bayanin ya kuma nuna cewa, a watan Janairu bankunan Nijeriya sun yi wa sabbin cibiyoyi 5,687 ragista da watan Fabrairu kuma an yi wa cibiyoyi 3,921 haka kuma a watan Maris an samu yi wa cibiyoyin PoS 7,585 ragista don ci gaba da gudanar da ayyukansu a fadun tarayyar kasar nan.
A watan Afrilu kuma ‘yan kasuwa sun samu yin ragistar wuraren gudanar da harkokin PoS har guda 8,537; 7,570 a watan Mayu kuma an samu 3,823 yayin da kuma a watan Yuni aka samu 1,351 sai watan Yuli na shekarar 2019 da aka samu 7,823.
Biniciken da hukumar NIBSS ta yi a fadin kasar nan ya kuma nuna cewa, an karbi ragistar cibiyoyin gudanar da PoS har guda 7,970 daga hannin bankuna a watab Agusta a watan Satumba kuma an samu cibiyar PoS 7,759 yayin da a watan Oktoba a kan samu yi wa cibiya 1,501 ragista, ‘yan kasuwa da cibiyoyin gudanar da kasuwanci masu zaman kansu ne suke a kan gaba wajen yin ragistar.
A watan Nuwamba aka fi samun cibiyoyin da aka yi wa ragista don kuwa an samu yi wa cibiya 10,532 haka kuma a watan Disamba na shekarar an yi wa cibiyoyi 9,400 ragista don gudanar da harkokin biya da karbar kudade.
Amma bayanan sun kuma bayyana cewa, cibiyoyi 61,821 aka rarraba don yin amfani da su na huldar kudade wannan ne ya kawo cibiyoyin PoS zuwa fiye da 217,283 ya zuwa watan Disamba na shekarar 2018.
Hakan kuma yanayin huldar amfani da fasahar PoS yana karuwa ne dai dai da yawan karuwar cibiyoyin PoS da ake da shi a wurare daban daban a fadin kasar nan.
A watan Janairu na 2018 an yi hulda na Naira Biliyan 152.099 wanda hakan na nuna anyi huldar kashi 67 fiye da Naira Biliyan 91.29 da aka tattara a watan Janairu na shekarar 2017.
A watan Fabrairu kuma na shekarar 2018 yawan huldar da aka yi ya karu zuwa kashi 61 na Naira Biliyan 90.2 in aka hada da abin a aka samu a shekarar 2017 na Naira Biliyan 144.88.
A watan Maris na shekarar 2018 an gudanar da hulda na Naira Biliyan 177.76 wanda ya nuna na samu fiye da kashi 70 fiye da na Naira Biliyan 104.48 da aka samu a shekarar 2017.
Bayanin ya kuma nuna cewa, a watan Afrilu na shekarar 2018 an gudanar da hulda Naira Biliyan 172.31 haka kuma ya haura abin da aka yi na hulda a daidai wannna lokacin da aka samu kashi 64 na Naira Biliyan 104.84 a daidai wannan watan na shekarar 2017.
An kuma an yi huldar Naira Biliyan 189.48 a cibiyoyin PoS na kasar nan a watan mayu na shekarar 2018 wanda haka ya haura abin da aka yin a hulda da kashi 70 a shekarar 2017 da ta gabata na Naira Biliyan 111.63.
A watan Yuni kuma huda a kafafen PoS ya karu da kashi 69 inda aka yin a kudi Naira Biliyan 107.66 a shekarar 2017 zuwa Naira Biliyan 181.827 a shekarar 2018.
‘Yan kasuwa sun yi hulda ta PoS na Naira Biliyan 185.04 a watan Yuli na shekarar 2018, hakan ya nuna an samu karuwar kashi 59 in aka hada da abin da aka sakmu a daidai watan na Naira 116.57 na shekarar 2017.
A watan Agusta na shekarar 2018 kuma na samu karuwar hulda na kashi 65 na Naira Biliyan 124.4 a shekarar 2017 da kuma Naira Biliyan 204.81 a shekarar 2018.
A watan Satumba na shekarar 2018 kuma lamarin hulda a PoS ya karu zuwa kashi 62 na Naira Biliyan 200.18 daga Naira Biliyan 123.58 a shekarar 2017.
An kuma yi hukdar Naira Biliyan 212.37 a cibiyoyin PoS a watan Oktoba na shekarar 2018 in aka hada da abin da aka samu a shekarar 2017 na Naira Biliyan 132.39 wanda haka na nuna ya kai kashi 60.
A watan Nuwamba kuma, an yi huldar PoS ya karu da kashi 70 na Naira Biliyan 135.18 zuwa Naira Biliyan 230.03.
Bayananin ya kuma nuna cewa, a watan Disamba huldar ya karu da kashi 62 na Naira Biliyan 167.58 a shekarar 2017 zuwa Naira Biliyan 271.95 a shekarar 2018.
Daraktan kamfanin ‘Global Accelered’ Mista Kayode Ariyo, ya ta’allaka wannan karuwar da aka samu ya faru ne saboda yadda jama’a suka karbi huldar kudade ta hanyar kafafen sadarwa na zamani.
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu an samu sabon yanayin da jama’a da dama suna karbar hanyar zamani na aikawa da karbar kudade haka kuma yana kara yawan cibiyoyin PoS a fadin Nijeriya.
Ya ce, “Babban dalilin da ya sa aka samu karbuwar PoS shi ne yadda jama’ar su ka kara amanna da hanyar biya da karbar kudade ta hanyar kafafan sadarwa na zamani.

Exit mobile version