Daga Muh’d Shafi’u Saleh,
Mutanen garuruwa da dama a Karamar Hukumar Girei ta Jihar Adamawa sun gudanar da zanga-zanga zuwa harabar Majalisar Dokokin Jihar bisa zargin da suke yi wa shugaban karamar hukumar ta Girei, Hon. Judah Amisa, da sayar musu da gonakin da suke nomawa tun iyaye da kakanni.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Yola, jagoran masu zanga-zangar, Ahijo Yakubu, ya ce, shugaban karamar hukumar ta Girei ya sayar da filayen da suke noma sama da kadada 10 ga kansila guda, yana kuma shirin sayar da wata kadada 500.
Ya ce, “filayen noma na mutane daban-daban da talakawa ke amfani da su wajan noma, su shugaban karamar hukumar Girei ya ke sayarwa.
“Yanzu haka sun kawo kokenmu gaban majalisar dokokin jiha akan shugaban karamar hukumar Girei, wanda siyasarsa ta zama barazana da cuta ga jama’a, yana yaudaran gwamnatin jiha wanjan kwace gonakanmu da muka gada daga iyaye da kakanni.
“Shugaban karamar hukumar Girei, ya zame mishi al’ada sayar da filayenmu ga wasu mutane, kuma ana baraanar kwacewa,” inji Ahijo.
Masu zanga-zangar sun bukaci majisar dokokin jihar da ta kwace filayen da su su ka rage a matsayin hanyar rayuwar talakawan da ke kauyokan karkarun.
Mutanen da su ka gudanar da zanga-zangar da ba su gaza mutum 40 ba, sun kasance maza da mata da su ka hada kabilu da dama na karamar hukumar Girei, kuma suna daga kwalaye da ke nuni da ‘ba mu yarda da sayar da filayenmu ba, a dawo mana da filin nomanmu kadada 500’.
Wasu daga cikin garuruwan da lamarin ya shafa sun hada da Gawu, Sauro, Daudo, Mokawu, Walare, Surutu da dai sauransu.
Yayin da yake magana da manema labarai shugaban karamar hukumar Girei Juda Amisa, ya ce filayen dama wurare ne da’aka ware a matsayin yankunan da gwamnati ta tanada, ya ce ‘yan siyasa ke ruru wutar batun.
Shugaban ya kuma bukaci masu zanga-zangar da su tantanci abinda su ke nema a ma’aikatar fili da safiyo, domin a tantance mu su.