Daga Muhammad Maitela, Damaturu
Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya jagoranci bambobin majalisar wajen karbar zagayen farko na gudanar da allurar riga-kafin cutar korona a zauren majalisar a ranar Talata.
Ofishin Sanata Lawan, a sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun mai taimaka wa shugaban majalisar kan harkokin yan jaridu, Mista Ola Awoniyi a Abuja.
Haka zalika kuma, ya ce likitan shugaban majalisar, Dr Muhammad Usman shi ne ya yi wa Lawan allurar a gaban idon sauran yan majalisun, a karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi.
Bayan kammala yi masa riga-kafin, shugaban kwamitin majalisar akan kiwon lafiya, Sanata Ibrahim Oloriegbe ya mika wa shugaban majalisar katin shaidar yi masa allurar.
Jim kadan da kammala riga-kafin cutar korona, Sanata Lawan ya yi kira ga yan Nijeriya su bayar da cikakken hadin kai tare da tabbatar an yi masu allurar riga-kafin.
Yayin da ya kada baki ya ce, “Annobar korona gaskiya ce, wadda har yanzu mu na fuskantar kalubalenta, saboda haka ina rokon yan Nijeriya, musamman wadanda su ke da shekarun da hukumomin kiwon lafiya su ka kayyade da kuma ma’aikatan lafiya da su je ayi musu wannan riga-kafin.
“Bugu da kari, duk da cewa yin allurar ganin dama ne amma ya kamata a yi wa kaso mafi yawan yan Nijeriya, domin cin galabar annobar.
“Kuma mu na bukatar wayar da kai tare da kokari wajen samar da allurar a dukkan lungunan kasar nan, wanda abin bai tsaya kawai inda ya ke da saukin shiga ba, dole a shigar da riga-kafin kowane sako a kasar nan.
“Har wala yau, akwai bukatar daukar ingantattun matakan fadakarwa da ilmantar da yan Nijeriya alfanun riga-kafin ta hanyar da zai kai ga sun amince. Sannan kuma ya kamata mu yi amfani da hanyoyin da ake amfani da su a baya wajen yi wa jama’ar mu allurar riga-kafi.
“Akwai bukatar shigar da sarakunan gargajiyar da malaman addini wajen bayar da gaggarumar gudumawa a fannin wayar da kan jama’a, saboda ko shakka babu wannan shi ne abinda ya kamata mu yi kenan, a matsayin Nijeriya wani bangare ce a duniya.
“Haka zalika kuma, na yi imani kan cewa daga karshe za mu samu garkuwa daga wannan annoba, a kokarin da ake dashi wajen ganin an yi wa kaso 70 na jama’ar da ake bukatar ayi wa riga-kafin.”
A hannu guda kuma, shugaban majalisar ya taya kwamitin shugaban kasa murnar samun nasara a yaki da cutar korona saboda aiki tukuru don samar da wannan allurar riga-kafin ga yan Nijeriya.
A karshe ya shawarci kwamitin ya yi kara kokarin adadin allurar riga-kafin samfur dabam-dabam ba sai AstraZeneca ba kawai.