Sabon fim ne, wanda ya zo da salon labari mai mutukar jan hankali.
Hakika ya zo da wani samfuri na musamman da ya sha bamban da a akasarin gama-garin fina-finan da aka saba yi, d’auke yake da kayan takaici, mamaki, cin amana, dambarwa iri daban-daban.
Abu ne mai mutukar mamaki idan babbar mace ta kamu da so da kaunar matashin saurayin da a haife ta haife shi. Irin hakan ne ta faru da wata a cikin fim d’in wanda ya farauci zuciyarta zuwa ga matashin wanda ba shi da aiki da ya wuce zaman banza da yaudara, wato wakili ne na wasu samarin yanzu (‘cima-zaune” a ta bakin shugaban kasa). Domin babban burinsa shi ne samun wata hanya da zai tsinci dami a kala ya samu gumakan zamani (kudi). Da zai yi facaka son ransa ya ci bulus!
Sai dai babban kalubale da ya zamo cikas a gare shi, Hajiyar mai son wuf da shi shi ne, babban d’anta abokinsa ne na cin mushe wanda suka jima da tattauna batutuwa akan samun auren da za su huta.
A d’aya gefen kuma ga iyayensa sun cinno masa wutar cewa ba zai yiwu ya aureta ba musamman mahaifiyarsa da ta fi daukan zafi a kansa. Sai kuma direban Hajiya Musa da ya yi tsalle ya dire cewa ai babu wanda ya dace da ta aura sai shi. kalubalen sun yi yawa, ga na iyayensa, na Dan Hajiya, na ‘yar Hajiya, na Direban Hajiya da dukkansu ba sa so. To, shin shi din ma yana son Hajiyar ne, to, wane irin so yake yi mata? Wace irin soyayya ma suke yi?
Mece ce irin rawar da malamai suke takawa ko fatawarsu a kai?
Ko ya abin yake kasancewa, sai ku biyo wannannn kayataccen shirin domin gani dai ya kori ji, ya tafi da salo mai karsashi da tsuma zuciyar mai kallo ya ji yana bukatar zama ya yi ta kallon fim d’in.
Shi kuwa Haruna Birniwa, marubucin littafin yabo na Zuwa Ga Sarkin Kano Sanusi II, ya bayyana dalili da hikimar sunan fim din:
Asalin kalmar ‘WUF’ tana nufin hanzari ko yin zafin nama ko fakar ido a yi maza a aikata abu, musamman kafin wani/wata/wasu su ankara, musamman wajen yin amfani da wata dama mai kurarren taki.
‘Wuf’ a yanzu kuma ta zama wata kalma ce da aka sabunta ta daga Hausawan wannan zamani ake amfani da ita yayin da wata mace mai shekaru ta auri saurayi mai kananun shekaru, ko kuma shi namijin mai tarin shekaru ya auri mace budurwa ‘yar fiririya wacce ba ta wuce sa’ar ‘yarsa ba ko jika.
Ana cewa wane/wance sun yi wuf da wani ne ga duk auren da ya zamana tsakanin dattijo/dattijuwa mai wata alfarma, kama daga kan tarin dukiya, matsayi, sarauta, mulki, daukaka ko launin fata na daban da kuma mace ko namijin da ke da karancin shekaru, musamman in yana da karancin dattin aljihu, wato kudi.
Shi wannan fim an gina shi ne bisa adabi kan doron addini da al’adar Hausawa, cikin zayyana dalilai da alfanun wannan sabon salo na Wuf da kuma yanda za a bi a kaucewa fadawa matsalar da ke cikinsa.
Shirin Wuf ya samu aiki daga kwararrun ‘yan wasa zuwa kan ma’aikatan da suka shirya tare da ba da umarni, don haka shirin Wuf shiri ne da ya cancanci kallon matasa da dattijai, ko malamai da attajirai, kai har ma da jami’an tsaro da ma’aikatan gwamnati.
Za a saki wannan fim din a manhajar YouTube ranar Laraba, 20 ga Janairu, 2021.
Yusuf Yahaya Gumel, shine Mataimakin Shugaba na kungiyar marubuta ta Jigawa State Writers Association (JISWA).