Gamayyar kungiyoyin fararen hula a Abuja, sun koka kan yadda gwamnatin tarayya ke kauda ido aka hukunta wasu jami’anta da ake zargin da cin hanci, lamarin da ke haddasa kokonto kan yaki da cin hanci da ake yi a kasar. Kungiyoyin kare hakin jama’ar sun gudanar da zanga-zanga da zaman dirshan na wasu sao’i a Abuja, bisa abin da suka bayyana damuwarsu kan rashin daukan matakin da shugaban kasar ke yi a kan batutuwa na cin hanci da rashawa da suke ganin lamarin na wuce gona da iri.
Su dai masu wannan zanga-zangar sun gudanar da wani zaman dirshan a dandalin yanci da ke Abuja, akan batutuwan da suka danganta da rashin daukar matakai da gwamnatin kasar taki yi akan masu cin hanci da rashawa da ake yi wa jami’an gwamnatin Najeriya.
Kama daga kan sakataren gwamnatin kasar da aka dakatar da shi bisa zargin almundahana, ta Naira Milyan Dari biyu da tsaba’in, wanda duk da mika rahoto ga bangaren gwamnatin amma shiru kake ji izuwa ga batun shugaban hukumar leken asiri, da shima aka gano tsabar kudi har Dala miliyan hamtsin shima din shiru kake ji kamar an shuka dusa.
Ga na baya-bayan nan na kamfanin NNPC na man fetur din Najeriya, da suka ce ta kai ga nuna wa juna yatsa tsakanin sa da Ministan kasar a ma’aikatar man, da shugaban kamfanin na NNPC, sannu a hankali sun ce ana neman mai da batutuwan na zargi-zargen cin hanci da ke faruwa a karkashin gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari wanda lamarin na neman zama wasan yara don haka baza su lamunta ba.
Commared Bako Abdul Hassan, shine shugaban kungiyar Campaign for Democracy, wanda yake Kaduna, yace “mun gaji da gafara sa bamu ga kaho ba, yau akwai abubuwan da suke faruwa game da tafiyan shugaban cin kasar nan, Janaral Muhammadu Buhari shugaban mu lokacin da ya hau mulki mun ga kowa ya nutsu, kowa ya dawo taitayin shi.”
“Amma daga baya mutanen da ya dauka suna aiki a tare da shi kamar Sakataren gwamnati almundahana na kudin jama’a da suka yi a NNPC, an dawo an zargi shi shugaban ‘yan sanda dan wannan abun zai shafi mutumcin shi mun san shi bame almundahana bane da dukiyan jama’a, to idan yasan bazai iya ba to ya yada kwallon mangoro ya huta.”
Masu zanga-zangar sun yi alkawarin ci gaba da zanga-zangar hade da zaman dishan har sai Baba ta gani a kowacce rana a dandalin yanci da ke Abuja. To amma basa ganin abubuwane da ake bincike akan su sannu a hankali. Commared Deji Adeyanju, jigo ne a kungiyar masu fafutuka akan wannan lamari ya ce.
“Maganganu da Ministan NNPC yayi wannan maganganun ne yasa hankalin mu ya tashi muka ce la irin wannan kudin mutum guda daya ne yazo ya bada kwangila, ba wanda ya sani, daga baya shekaran jiya muka ji Presidency suka fito suka ce ba wani magana, miliyan ashirin da biyar wai babu wannan maganan haka.
“Sai mu ka ce indai babu maganar haka to ya kamata Buhari ya sauke shi daga matsayin sa na Minista , to abubuwan nan bai faru ba har zuwa yanzu da nake wannan maganar, mun fitone domin shugaban kasar mu ya dauki mataki akan wannan maganganun tun shekarar da ya wuce har akan Babati Lawan, babu wani mataki da aka dauka saboda shugaban kasa ya rufe kunnen shi. Wannan ba daidai bane wannan abun ya koma kamar rainin hankali.”
Abin jira a gani shine ko zanga-zangar da zaman dirshan irin wannan zai samu dorewa dama yin tasiri na samun sauyi daga bangaren gwamnatin. Domin ta hanzarta fitar da sakamakon rahotanni na bincike-binciken da aka gudanar akan zargin cewa jami’an da ke aiki a karkashin ta sun aikata ba daidai ba, a amanar da aka mika musu.