A jiya Litinin ne, aka yiwa shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo allurar riga kafin farko na COVID-19, da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar, kamar yadda jam’iyyar PDGE mai mulkin kasar ta bayyana a shafinta na Intanet
Yayin bikin yiwa shugaban allurar rigakafin na kasar Sin, Obiang, ya yi kira ga al’ummar kasar, da su karbi rigakafin, kasancewar ita ce hanya daya tilo, da za ta magance mace-mace dake da nasaba da annobar.
Shafin Intanet na jam’iyyar PDGE, ya ruwaito shugaba Obiang, na bayyana kasar Sin a matsayin aminiyar Equatorial Guinea da kuma nahiyar Afirka.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana cewa, a ranar Larabar da ta gabata ce, wani rukuni na alluran rigakafin annobar COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya isa Malabo, babban birnin kasar, abin da ke zama kashin farko na tallafin alluran rigakafin da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)